✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu rufe rajistar masu zabe a karshen watan Yuli —INEC

Kotu ta kori karar da Kungiyar SERAP ta shigar gabanta.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ce za ta rufe rajistar masu kada kuri’a a ranar 31 ga watan Yulin da muke ciki.

Babban Kwamishinan INEC, Festus Okoye ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja, babban birnin kasar.

Matakin na zuwa ne bayan da wata Babbar Kotu a Abuja ta kori karar da Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci ta shigar gabanta.

Kungiyar ta SERAP dai na neman kotun ta tilasta wa INEC kara wa’adin rajistar da ke gudana a fadin kasar.

Okoye ya ce kotun ta tabbatar da cewa INEC na da damar sanya ranar rufe rajistar kamar yadda sabuwar Dokar Zabe ta 2022 ta tanada.