✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za mu sama wa Katsina N10bn daga hasken rana a shekara —NNPP

Jam'iyyar NNPP ta yi alkawarin samar da kudaden shiga Naira biliyan 1o daga hasken rana a duk shekara a Jihar Katsina.

Dan takarar Gwamnan Katsina a Jam’iyyar NNPP, Nura Khalil, yi alkawarin tara kudaden shiga Naira biliyan 10 daga hasken rana a duk shekara a jihar.

Injiniya Nura Khalil ya ce kudaden shigar N10bn da jihar za ta rika samu daga bangaren hasken rana zai sa ba sai ta jira daga Asusun Tarayya ba.

A jawabinsa a taron fara yakin neman zabensa a Karamar Hukumar Mashi, ya ce, “Na fara da Mashi ne saboda da ita da Daurawa ta Jihar Jigawa da Kankiya bisa ga binciken da muka yi sun fi samar da hasken rana da za ta samar da lantarki ba sai an jira daga wani wuri ba.

“Za mu yi amfani da wannan hasken wutar lantarkin don sama wa jihar kudaden shigar da akalla za a samu bilyan N100 a shekara.

“Kudaden za mu yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan gwamnati ba sai mun jira na Gwamnatin Tarayya ba.”

Ya kara da cewa idan ya ci zaben da ke tafe a watan Maris,  “Muna da shirin kafa banki mallakar gwamnatin jiha wanda zai iya bayar da damar yin ajiya mai kama da shirin adashe don dai mu farfado da tattalin arzikin jihar.”

Game da matsalar tsaro, dan takarar ya ce Katsina tafi sauran jihohi hadari, amma idan NNPP ta hau mulki zai zama tarihi.

Ya kuma yi shagube ga wadanda yake zargi da sayen katinan zabe da nufin yin magudin zabe, da cewa a wannan karon karyarsu a kare.

“Ana bin mata ana sayen katunan zabensu a kan N10,000 amma a karshe sai a ba su N500.

“To a sani, babu batun magudi a wannan zaben, balle a ba wani katin wani ya je ya jefa kuri’a sama da goma,” in ji shi.

Ya zargi gwamnatin APC ta Jihar Katsina da yin watsi da fannin ilmi; inda ya ce a shekara bakwai na gwamnatin, yara 100,000 sun kasa rubuta jarabawa.

Don haka ya bukaci jama’a su zabi Jam’iyar NNPP don ta fitar da su daga kunci da rashin tsaron a jihar.

Tun da farko shugaban NNPP na jihar Katsina, Sani Liti ’Yankwani, ya ce, matsalolin satar jama’a, kisa da jahilci, sun ishi mutane hankali, saboda abin da ya kira rashin kulawar gwamnatin jihar.

A kan haka ne a ce idan aka zabi NNPP, za ta kawo karshen matsalolin musamman na rashin tsaro.

Shugaban NNPP na Kasa kuma dan takararta na shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya dan takarar Gwamnam Kano na jam’iyar, Abba Kabir Yusuf (Abba gida-gida) ya wakilta, ya ce, jam’iyy ta yi kyawawan tanade-tanaden samar da ayyukan yi da tallafin sana’o’i ga mata da matasa da kuma kawo karshen matsalar tsaro.