✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu shiga wani hali matukar ba a takaita yawan haihuwa ba – Sanusi

Sanusi ya ce bai kamata iyaye su haifi 'ya'yan da ba za su iya kula da su ba.

Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya yi kira da a fara aiwatar da cikakkun dokokin kayyade iyali domin takaita yawan al’ummar Najeriya.

Sanusi na wadannan kalaman ne ranar Laraba a wurin taron tattalin arziki na Ehingbetti da yake gudana a Legas, yana mai cewa kamata ya yi iyaye su haifi ‘ya’yan da kawai za su iya kula da su.

A cewar tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasa na CBN din, alkaluma na nuna cewa gwamnati ita kadai ba za ta iya samar da isassun abubuwan raya kasa da za su wadatar yaran da ake haifa yanzu haka ba.

Daga nan sai ya zargi halin da kasar ke ciki kan tsarin dokokin da ake amfani da su a kasar inda kowa zai iya haifar ‘ya’ya barkatai, ko da kuwa ya san ba shi da ikon daukar dawainiyarsu.

Ya ce ko da a Shari’ar Musulunci hakan ba daidai ba ne.

Sanusi ya ce “Maganar cewa mutane za su iya aurar mata ko nawa ne ba tare da doka ba, sannan su haifi ‘ya’ya ko nawa ne ba tare da za su iya ciyar da su kuma su ilimantar da su ba, ba daidai ba ne ko a Musulunce.

“Ban san me ya sa ba, amma akwai wata irin gurguwar fahimta akan aiwatar da irin wadannan dokokin a Musulunce, domin shi kansa addinin bai goyi bayan kawai ka tara iyalan da ba za ka iya daukar nauyinsu ba.”

Bai kamata mutane su haifi ‘ya’yan da ba za su iya kula da su ba

“Za mu iya ci gaba da wa’azi kuma muna shawartar gwamnati ta kara ware kudade a harkar ilimi, amma muddin mutane za su rika haifar ‘ya’ya 20 ko 30 ba tare da za su iya ilimantar da su ko tarbiyyantar da su ba, to hakika gwamnati abin zai fi karfinta.

“Ba wai kawai bukatar kashe kudade a kasafin kudi ake ba, a’a akwai bukatar canza tunanin mutane sannan a kawo dokokin da za su canza su kafin a magance wannan matsalar,” inji shi.

Daga nan sai tsohon Sarkin ya yi kira ga ‘yan Najeriya kan su rungumi tsarin iyali da kuma bayar da tazarar haihuwa a matsayin muhimman hanyoyin tsara ci gaban kasa.