✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu tura wakilai su sa ido a shari’ar Kanu – Ohanaeze

Ohanaeze ta ce wakilan za su sa ido su tabbatar an yi wa dan nasu adalci.

Kungiyar nan mai rajin kare muradun ’yan kabilar Ibo, Ohanaeze Ndigbo ta ce za ta tura wakilai da za su sa ido a shari’ar shugaban haramtacciyar kungiyar nan ta ’yan awaren Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu.

A cikin wata takardar bayan taro da ta fitar bayan taron Majalisar Zartarwarta ranar Lahadi, kungiyar ta ce wakilan za su kasance karkashin jagorancin mai ba ta shawara kan harkokin shari’a da kuma wasu fitattun ’yan kabilar ta Ibo.

Takardar dai na dauke ne da sa hannun kakakin kungiyar, Alex Ogbonnia.

Ohanaeze ta kuma ce ta damu matuka kan korafin ’yan kabilar, musamman matasa kan cewa ba a damawa da su a harkokin kasa, matsalar kalubalen makiyaya da sauran batutuwan da suka addabe su.

Daga nan sai ta yi kira ga matasanta da su kasance masu bin doka kuma su kyale shugabanninsu da sauran masu ruwa da tsaki su magance matsalolin nasu cikin ruwan sanyi.

“Duk da cewa kungiyarmu ba wai ba ta goyon bayan shari’a ba ne, amma ya zama tilas a yi masa shari’ar cikin dokokin tarayyar Najeriya, kamar yadda dokokin kasa da kasa suka amince da su.”

Sanarwar ta kuma ce Ohanaeze na tare 100 bisa 100 da matsayin da Kungiyar Gwamnonin Kudancin Najeriya ta dauka a kan hana kiwo, sake fasalin kasa, mayar da mulkin kasa zuwa yankin a 2023, da kuma batun ba wa yankin da ke da arzikin man fetur kaso biyar cikin 100 na kason kudin.

“Muna tare da matasa ’yan kabilar Ibo kan korafe-korafensu kan nuna musu wariya, matsalar makiyaya da dai sauransu. Sai dai ba ma goyon bayan tayar da zaune tsaye wajen kalubalantar wadannan batutuwan,” inji Ohanaeze.

 

A cewar sanarwar, “Kungiyar Ohanaeze ta lura matuka da yadda aka sake kama danmu, Nnamdi Kanu kuma ake kokarin sake gurfanar da shi a gaban kotu.