✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu yaki sayen kuri’a a zaben Osun —Jami’an tsaro

Jami'an tsaro sama da 23,100 ne aka tura Jihar Osun don ba da kariya yayin zaben gwamnan jihar da zai gudana a Asabar mai zuwa.

A matsayin wani bangare na kokarin ganin an gudanar da zabe mai tsafta a Jihar Osun, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun tare da sauran hukumomin tsaro a jihar, sun ce ba za su sassauta wa masu hakar sayen kuri’u’a ba a zaben gwamnan jihar da ke tafe.

Rundunar ta ce sun fitar da wasu tsare-tsaren da za su taimaka musu wajen yaki da masu sayen kuri’un a yayin zaben.

Don cim ma wannan kuduri, rundunar ta ce an tura jami’ai, ciki har da jami’an farin kaya wadanda za su sanya ido kan yadda harkokin zaben za su gudana.

A ranar Asabar ake sa ran gudanar da zaben gwamnan jihar, inda al’ummar jihar za su zabi wanda zai ja ragamar mulkin jihar na shekara hudu masu zuwa.

Sayen kuri’u al’ada ce da aka saba gani a lokutan zabe a Najeriya, inda wakilan jam’iyyu kan yi amfani da damar wajen nema wa ’yan takararsu kuri’u.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’an tsaron sun yi kyakkyawan shiri domin hana faruwablr irin abin da ya faru a Jihar Ekiti a zaben Osun.

Jami’an tsaro sama da 23,100 ne aka tura zuwa Jihar Osun don ba da kariya yayin zaben gwamnan jihar da ke tafe.