✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu yi maganin ’yan bindiga a Zamfara — Matawalle

Gwamnan ya sha alwashin zakulo wanda suke daukar nauyin ayyukan 'yan bindiga a jihar.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa za ta sa kafar wando daya da wanda suke daukar nauyin ayyukan ’yan bindiga a jihar.

Ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin da yake bayani a talabijin ga jama’ar jihar a Gusau, kan yadda hare-haren ’yan bindiga ke ci gaba da kamari a jihar.

“Makonnin da suka gabata an samu hare-haren ’yan bindiga da dama, duk da kokarin da muke na kawo karshen matsalar.

“Maharan na kashe mata, yara, tsofaffi babu wani tausayi kuma sanadiyar haka a kullum daruruwan mutane ke kaura daga garuruwansu don tsira da rayuwarsu.

“Idan za a tuna a farkon gwamnatinmu mun yi kokarin samar da hanyoyin wanzuwar zaman lafiya a jihar nan,” a cewar Matawalle.

Gwamnan ya tabbatar da zai ci gaba da jajircewa wajen daukar mataki kan wanda suke daukar nauyin ayyukan ’yan bindiga a jhar.

“Abun mamaki abubuwa a yanzu na ci gaba da ta’azzara wanda kuma ba zamu lamunta ba.

“A bayyane abun yake cewar akwai wanda suke daukar nauyin ta da hankulan mutanen jihar tsawon shekaru, ina kuma addu’ar Allah ya tona asirin duk wanda ba ya son zaman lafiyar jama’armu.

“Ina tabbatar da muku da cewar za mu ci gaba da zage damtse wajen yaki da ta’addanci da dukkan wasu laifuka a jihar nan,” a cewarsa.

Sannan ya ja hankalin jama’ar jihar da su hada kai da jami’an tsaro wajen bayar da bayanan sirri da su taimaka wajen yaki da ta’addanci a jihar.