✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zabar Atiku a matsayin mataimakina kuskure ne —Obasanjo

Daya daga cikin kura-kurai da na tafka shi ne na zabi Atiku a lokacin da nake son zama Shugaban Kasa.

Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce daya daga cikin kura-kuran da ya yi a rayuwa shi ne zaben tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar a matsayin abokin takararsa a Babban Zabe na 1999.

Ya bayyana hakan ne a wani taron baje-kolin littafai da aka gudanar a Dakin Karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL) da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Da yake amsa tambayoyin daliban sakandiren da suka yi baje-kolin littafai da aka gudanar ranar Asabar, Obasanjo ya bayyana yadda dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da Atiku a lokaci da suke neman wa’adi na biyu gabanin Babban Zabe na 2003.

A yayin bayyana tarihin rayuwarsa da nasarorin da ya samu a lokacin da yake Shugaba na zamanin mulki soji da na farar hula, ya ce ya tafka kura-kurai da dama a rayuwarsa, amma a kusan kowane lokaci Allah Yana bashi nasara kuskuren ba ya tasiri.

Tsohon Shugaban kasar ya ce, “Daya daga cikin kura-kurai da na tafka shi ne na zabi Atiku a lokacin da nake son zama Shugaban Kasa, amma saboda kuskure ne da na aikata da zuciya daya, sai Allah Ya kubutar da ni.

“Kuskure na biyu shi ne lokacin da tsohon Shugaban Kasa Abacha ya so kama ni, sai Jakadan Amurka a wancan lokaci ya sanar da ni halin da ake ciki, amma ya ce da ni Amurkan za ta bani mafaka. Sai na ce a’a hakan zai iya zama kuskure wanda da na amince zan iya rasa rayuwata.

“Saboda haka zan iya cewa akwai abubuwa da dama wadanda kuskure ne amma Allah Yana bani ikon tsallake dukkansu.”

Ya kamata matasa su karbe madafun iko a kasar nan

Obasanjo ya koka kan yadda aka sake maimaimata tsofaffin ‘yan siyasa a mukamai, yana mai cewa matasan Najeriya ba za su taba samun damar karbar madafun iko ba a kasar nan muddin aka ci gaba da tafiya a haka.

Da yake ci gaba da bayani kan damar da matasa ke da ita na karbe ragamar jagoranci a kasar, Obasanjo ya kuma bayyana damuwa yadda kudi ke tasiri wajen tafiyar da al’amuran siyasa a kasar, yana mai cewa hakan zai zame wa matasan babban kalubale.

Sai dai ya shawarci matasan a kan kada su debe tsammanin cewa za su karbe madafun ikon kasar duk da yadda kudi su ne masu gidan rana a harkokin siyasar kasar.

Ya ce duk da wannan yekuwar ta “Not Too Young to Run”, idan aka duba a yanzu galibin ’yan takara ’yan tsakanin shekara 70 zuwa 80 ne, “saboda haka ta yaya za a yi matasa su samu dama”?