✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zabe: Ku mutunta ’yancin ’yan Najeriya —Alkali ga ’yan sanda

Ya gargadi 'yan sanda da su nuna nagarta a lokacin zabe.

Babban Sufeton-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya gargadi ’yan sanda da aka tura domin gudanar da aikin zabe mai zuwa da su mutunta ’yancin ’yan Najeriya.

Ya yi wannan jawabi ne a Abuja a ranar Litinin a wajen fara wani horo da rundunar tare da hadin gwiwar ‘Central Soft Support Services Limited’ suka shirya.

“Dole ne mu mutunta hakkokin ’yan kasa masu bin doka da oda sannan mu binciki wadanda ke son kawo akasin haka”, in ji shi.

Baba ya kuma yi kira ga sauran hukumomin tsaro da su nuna halaye masu kyau a wajen aikin zaben, inda ya ce ya kamata a bar ’yan kasa su yi amfani da ikon da suke da shi wajen yin zabe cikin lumana.

An shirya horon ne ga ’yan sanda da sauran jami’an tsaro don sanin makamar aiki game da zaben da zai wakana a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Baba, ya ce an shirya horon ne bisa la’akari da irin nauyin da ya rataya a wuyan jami’an tsaro don samar da yanayi mai kyau ga ’yan kasa domin su yi amfani da damarsu.

“Muna da muhimmiyar rawar da za mu taka la’akari da cewa muna da abubuwan da za mu iya fuskanta a matsayinmu na hukumomin tsaro.

“Na farko, dole ne mu ’yan sanda kada mu zama abokan gaba, ko a yi amfani da mu wajen yin zagon kasa.

“Na biyu kuma, dole ne mu samar da yanayi mai kyau ga ’yan Najeriya da ke son yin amfani da ikonsu don zabar shugabannin da suke so.”