✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023 ba zai tabbata ba muddin babu tsaro a Najeriya — PDP

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, ta ce zaben 2023 ba zai tabbata ba matukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta kawo karshen matsalolin tsaro…

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, ta ce zaben 2023 ba zai tabbata ba matukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta kawo karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta ba a yanzu.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus ne ya bayyana hakan yayin wani taron majalisar kolin jam’iyyar da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito Secondus yana cewa, akwai bukatar Shugaba Buhari da jam’iyyarsa ta APC su gaggauta kiran taro kan tsaron kasa da zummar kawo karshen matsalar da ta dabaibaye kasar nan.

Ya ce, “matsalolin tsaro sun durkusar da kasarmu sannan babu wani mataki daga gwamnati duk da cewa samar da aminci shi babban nauyi da rataya a wuyan kowace gwamnati ta hanyar tabbatar da tsaro al’umma.

“A baya ayyukan ’yan bindiga ya takaita ne ga Arewa maso Gabas, amma yanzu kauyuka 50 ne a karkashin ikonsu a jihar Neja kuma wurin da suke ma a yanzu mun ji labarin cewa ba shi da nisa daga Abuja.

“Fulani makiyaya sun addabi jihohin Yammacin kasar nan, ’yan bindiga na barna a Gabashi da Kudancin kasar duk suna kashe-kashe da sace-sace da kona gidaje.

“Al’amarin ya munana a yayin da ’yan Najeriya ke zaune cikin firgici,” in ji Secondus.