✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben 2023: Bai kamata a rika isgilanci da shugabancin INEC ba

Duk wasu kiraye-kiraye na a cire Shugaban INEC a wannan lokaci tamkar dauke hankalin al’umma ne, kuma zai rage wa zaben inganci.

Aranar Lahadin makon jiya ne Kungiyar ’Yan Arewa Masu Rajin Tabbatar Kyakkyawan Shugabanci ta yi kiran a cire Shugaban Hukumar Zabe (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu.

Kungiyar ta ce ta yi wannan kira ne saboda tsoron cewa da gangan Shugaban Hukumar Zaben da sauran ma’aikatan hukumar suke kokarin kassara muradun Arewa ta hanyar rage kuri’un yankin a zaben 2023 mai zuwa, zargin da ba ya da tushe bare makama.

Shugaban Kungiyar, Alhaji Mohammed Adamu ya kuma zargi shugabancin hukumar da ‘saba ka’ida’, inda ya ce hakan yana nunawa a fili cewa, hukumar ba za ta iya gudanar da sahihin zabe ba a 2023.

Har ila yau, sun bukaci a kama tare da gurfanar da Shugaban Hukumar Zaben ‘saboda yana kokarin amfani da ofishinsa wajen murde zabe.’

Bukatar cire Farfesa Yakubu ta bayyana a ranar 15 ga watan Satumba, 2022, lokacin da Kungiyar Jam’iyyun Kasar nan, ta ce, ta bankado wata kara da aka kai Hukumar INEC a Babbar Kotun Tarayya da ke Owerri a Agustan bana, inda aka bukaci a hana hukumar amfani da na’urar tantance masu zabe a zaben 2023.

Ba tare da bayyana wanda ya kai karar ba, Kakakin Kungiyar Jam’iyyun Kasar nan, Ikenga Ugochinyere ya yi ikirarin cewa, muddin aka yi nasarar hana amfani da na’urar tantance masu zabe ko Shugaban INEC ya ba da kai bori ya hau, to shirin cire shi zai tabbata.

An kara bankado kulle-kullen a ranar 12 ga watan Oktoba, 2022, lokacin da Shugaban Kungiyar Jam’iyyun ya bayyana cewa, ana yunkurin cire Farfesa Yakubu ne don a samu damar yi wa na’urar tantance masu zabe kutse ko a kashe ta daga uwar garken manhajar hukumar, ta yadda ba za a iya aika sakamakon zaben 2023 ba.

Wani abin takaici kuma shi ne, a ranar 13 ga Oktoba, jaridar Daily Trust ta yi rahoto cewa, ‘manyan ’yan siyasa da wasu mutane da suke da kusanci da Fadar Shugaban Kasa suna kulle-kullen yadda za a cire Shugaban INEC, muddin hukumar ta ki amincewa da bukatunsu na yin magudi a zaben.

Rahoton ya bayyana cewa, masu yin kulle-kullen suna son su ga an kawar da na’urar tantance masu zabe da fom din bayyana abubuwan da suka faru da kuma aika sakamakon zabe ta hanyar na’ura daga matakan zaben.

Haka rahoton ya ambaci wasu gwamnoni biyu da kuma wani kusa a Majalisar Dokoki ta Kasa a matsayin wadanda suke gaba-gaba a wadannan kulle-kulle, domin yin wasa da shugabancin Hukumar INEC da ma dimokuradiyyar Najeriya.

Wannan ba shi ne karo na farko ba da ’yan siyasa da ’yan kanzaginsu suka yi yunkurin ganin an cire Shugaban Hukmar Zabe ba, kafin zabe.

Gabanin zaben 2015, an bankado kulle-kullen cire Shugaban INEC na wancan lokacin, Farfesa Attahiru Jega, inda Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, ba ya da niyar yin hakan.

Haka a lokacin gabatowar zaben 2019, wasu kungiyoyi wadanda suka hada da Kungiyar Shugabannin Kudu da na Tsakiyar Kasar nan da Shugaban Jam’iyyar PDP na wancan lokaci, Yarima Uche Secondus da Shugaban Kungiyar Jam’iyyun Kasar nan sun yi ikirarin cewa, Shugaba Buhari yana kulle-kullen cire Shugaban INEC, inda shi ma ya fito fili ya musanta zargin a ranar 18 ga Fabrairun 2019.

Don haka, muna Allah wadai da irin wadannan kulle-kulle na ’yan siyasa da ’yan barandansu.

Dole ne a daina irin wadannan zarge-zarge marasa tushe.

Duk wasu kiraye-kiraye na a cire Shugaban INEC a wannan lokaci tamkar dauke hankalin al’umma ne, kuma zai rage wa zaben inganci.

Hukumar INEC ta sha bayyana aniyarta ta gudanar da sahihin zabe a 2023, inda zabubbukan da ta gudanar a baya-bayan nan suka tabbatar da hakan. Haka shi ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha bayyana aniyarsa ta tabbatar da sahihin zabe a matsayin daya daga abubuwan da za a rika tunawa da shi a kasar nan.

Saboda haka, bai kamata wasu ’yan siyasa masu bukata ta kashin kai su kashe masa gwiwa ba.

Ya kamata a kyale Farfesa Yakubu ya mayar da hankali wajen kula da harkokin zabe da tabbatar da sahihin zabe, ta yadda ba za a samu wani katsalandan ko cin zarafin masu zabe ba.

Kuma duk masu kira ga Shugaban Kasa ya cire Shugaban INEC sun manta cewa, Shugaban Kasa ba ya da ikon yin hakan bisa kundin tsarin mulkin kasa.

Sashi na 157 da 158 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (da aka gyara) sun bayyana sharudan cire Shugaban INEC da kwamishinonin hukumar da ’yan kwamitin gudanarwa na hukumomi tara.

Sashi na 157 ya ce, “Bisa tanadi na karamin sashi na (3) na wannan sashi, duk wani mai rike da wani mukami da ya yi daidai da tanadin wannan sashi, Shugaban Kasa zai iya cire shi ne kawai daga mukaminsa idan aka samu goyon bayan biyu bisa uku na ’yan Majalisar Dattawa, saboda ya kasa gudanar da aikin ofishin ko kuma rashin da’a.’’

A nan Hukumar INEC tana cikin hukumomin da aka zayyano a karkashin wannan sashi na kundin tsarin mulki.

Saboda haka, idan wani ko wata kungiya na zargin Shugaban INEC da rashin da’a, kamata ya yi ya bi matakan da kundin tsarin mulki ya zayyana, sannan ya mika kukansa ga hukumar da take da ruwa-da-tsaki, ta yadda doka za ta yi aikinta.

Duk wani abu akasin wannan, ya zama tamkar yin fito-na-fito ne da tsarin dimokuradiyyar Najeriya.