✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023: Bani da asara don Jam’iyyar APC ta fadi a Jigawa —Gwamna Badaru

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya koka dangane da yadda ake fama da rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar APC reshen Jihar da cewa ba…

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya koka dangane da yadda ake fama da rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar APC reshen Jihar da cewa ba za ta kwashe lafiya ba matukar a ci gaba da tafiya haka.

Gwamnan yayin kaddamar da kwamitin rikon jam’iyyar a ranar Juma’a 25 ga watan Disambar 2020, ya ce muddin jam’iyyar ba ta zauna lafiya ba to babu shakka hakan na iya janyo mata shan kasa a zaben 2023.

Gwamnan ya bayyana cewa kasancewarsa dan kasuwa, ba zai yi wata asara ba ko da kuwa jam’iyyar ta fadi zabe a Jihar matukar ba a yi aiki da lura ba an daina tayar da fitintinu a cikinta.

Jihar Jigawa na daga cikin jihohin da jam’iyyar APC mai ci a Najeriya ke mulki a jihar, kuma guda cikin jihohin da suke fuskantar barazanar faduwar zaben 2023, sakamakon rikece-rikicen cikin gida da ka iya kaita ya baro ta a zabe mai zuwa.

Gwamna Badaru wanda jigo ne a jam’iyyar APC a matakin kasa da kuma jihar Jigawa, ya lura cewa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a yanzu na iya zama babban kalubale da zai janyo mata shan mugun kaye a zaben mai zuwa.