✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023: Gwamnati ta ba jami’o’in Najeriya hutun mako 3

An dauki matakin ne domin bai wa ma'aikata da dalibai damar kada kuri'a

Gwamnatin Tarayya ta bai jami’o’in Najeriya umarni su rufe daga ranar 22 ga Fabrairu zuwa 14 ga Maris saboda zabubbukan da za a gudanar ran 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris, 2023.

Gwamnati ta ba da umarnin ne domin bai wa dalibai sama da miliyan 3.8 suka yi rajistar zabe damar kada kuri’a a lokacin zabuka masu zuwa.

Umarnin na kunshe ne cikin sanarwa mai dauke da kwanan watan uku ga watan Fabrairu wadda Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta aike wa jami’o’in fadin kasar.

Cikin sanarwar mai dauke da sa hannun Mataimakin Sakataren hukumar a sashen gudanarwa, Dokta Chris Maiyaki, NUC ta ce kare ma’aikata da dalibai da kadarorin gwamnati na daga cikin dalilan da suka sanya daukar wannan mataki.

“Duba da yadda lamurra ke tafiya da kuma damuwa da batun tsaron ma’aikata da dalibai da kadarorin gwamnati a jami’o’i, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bai wa daukacin jami’o’i da cibiyo masu alaka da su umarni kan su rufe daga 22 ga Fabrairu zuwa 14 ga Maris, 2023,” in ji sanarwar.

NUC ta ce kafin daukar wannan mataki sai da Ministan  ya nemi shawarwari daga hukumomin tsaron da suka dace.

Ya zuwa ranar 25 ga Fabrairu ake sa ran gudanar da zaben Shugaban Kasa na ‘yan Majaliusar Tarayya, yayin da na gwamnoni da na majalisun jihohi za su biyo baya a ranar 11 ga Maris, 2023.