✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023: INEC ba ta dan takara —Yakubu

Ya ce INEC ba jam'iyya ba ce

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta jaddada cewa babu wani dan takara ko jam’iyya da za ta mara wa baya a zaben 2023 mai karatowa.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce babu wani abu a gaban hukumar da ya wuce tsare-taren zabe.

“INEC ba jam’iyya ba ce, ba ta da dan takara a zaben. Abin da muka sa Baga bai wuce tsare-tsaren zabe ba.”

Ya bayyana haka ne lokacin da yake yi wa wasu jami’an da INEC ta nada (SPOs) don aikin zabe mai zuwa jawabi a Abuja.

A  cewarsa, “Hukumar na da yakinin gudanar da zabe mafi inganci a 2023, kuma ku ne mutanen da za ku taimaka wa hukumar wajen cim ma nasarar hakan.

Yakubu ya bayyana aikin jami’an a matsayin mai matukar muhimmanci wajen tabbatar da nasara a zaben na 2023.

Don haka ya yi kira a gare su da su tsare gaskiya da mutunci yayin zaben.

(NAN)