✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023: INEC ta soma yi wa ’yan Najeriya rajista

Sabon tsarin gudanar da rajistar ya kankama a wasu jihohin kasar.

A Litinin da ta gabata ce Hukumar Zabe a Najeriya INEC, ta sake bude rumfunanta domin ci gaba da yi wa ’yan kasar rajista ta hanyar amfani da yanar gizo.

Sanarwar da Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu ya fitar ta ce, wannan na daga cikin shirye-shiryen da ta assasa da zummar tunkarar babban zaben kasa na 2023 da ke tafe.

A cewarsa, suna fatan yi wa ’yan Najeriya miliyan 20 rajistar cikin shekara guda, a yayin da suke da burin ganin an yi wa ’yan kasar akalla miliyan 100 rajista gabanin babban zaben kasar.

“Yin rajistar ’yan Najeriya shi ne babban aikin da Hukumar ta sa a gaba, saboda haka INEC ta gabatar da sabon tsarin da zai bada damar yin rajista ta hanyar amfani da yanar gizo.

“Hakan zai bai wa kowane dan Najeriya da ba ya da rajistar damar samun rajistar wadda za mu dauki tsawon shekara guda muna gudanar da ita,” a cewar Yakubu.

Rahotanni sun ce sabon tsarin gudanar da rajistar ya kankama a wasu jihohin kasar kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.