✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023: Kalubalen da ke gaban Saraki

Saraki ya shiga jerin masu neman takarara shugaban kasa a zaben 2023

A kwanakin baya ne tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya shiga jerin manyan ’yan siyasar da suke da burin neman tsayawa takarar Shugaban Kasa a badi.

Saraki, wanda ya yi wa’adi biyu a matsayin Gwamnan Jihar Kwara, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana niyyarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin Jam’iyyar PDP.

A rubutun ya ce, “Yayin da muke shirin tunkarar tafiyar da ke gabanmu, ina fata za mu hada karfi da karfe don samun tikitin babbar jam’iyyarmu ta PDP, don mu hadu wajen gina kasa da za mu ji dadinta baki daya.

“Ku zo mu hada hannu don al’ummarmu ta samu sauki da kuma aminci, wannan wata dama ce a gare ku da ku da danginku. Ina da tanadi mai karfi da na shirya, kuma ina da gogewa wajen ganin al’amura sun inganta.

“Bari mu samar da sabuwar Najeriya da za ta yi aiki don ci gaban kowa da kowa!”

Saraki shi ne tsohon Shugaban Majalisar Dattawa na biyu da ya bayyana niyyarsa ta neman wannan kujera ta a kasar nan.

Da farko dai tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Anyim Pius Anyim, ya bayyana niyyarsa ta neman tsayawa takara a Jam’iyyar PDP.

Tsohon Gwamnan Jihar Kwarar ya shiga sahun masu neman tikitin PDP a takarar, inda ya shiga cikin masu son takarar da suka hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, sai tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da wadansu da dama da ko dai suka bayyana niyyar tasu ko ana hasashen suna da niyyar yin takarar Shugaban Kasar.

Tun kafin sanarwar tasa a hukumance, kwamitin yakin neman zaben Saraki na kasa a karkashin jagorancin Farfesa Hagher Iorwuese, ya yi zagaya sassan kasar nan, domin neman albarkar wadanda abin ya shafa a fagen siyasar Najeriya don goyon bayan takarar gwanin nasu.

Daya daga cikin wannan yunkuri shi ne ziyarar da suka kai wa Cif Edwin Clark da tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida inda ya kwatanta Saraki da wanda ya san makamar mulki, mai kuma juriya da sadaukar da kai don ci gaban kasa.

“Kun zakulo wanda ya dace da shugabancin kasar nan. Muna bukatar shugaba wanda zai iya amfani da ɗimbin arzikinmu don amfaninmu.

“Wanda zai magance mana nuna bambanci da kuma rugumar kowa a tafi tare don bunkasa kasar nan.

“Na yi imanin cewa Saraki zai iya dawo da wannan daukaka ga al’ummarmu. Kuma ina yi masa addu’a, da kuma ba shi cikakken goyon baya na,” inji Janar Babangida.

Sai dai a yayin da ayarin magoya bayan Saraki ke samun gindin zama na tsayawa takararsa, wasu batutuwa na iya kawo cikas ga burinsa na zama Shugaban Kasa.

Batun shiyya-shiyya

Batun raba manyan mukamai a zabe babban batu ne a siyasar Najeriya. Duk da cewa ba ya cikin kundin tsarin mulki, ana kallonsa a matsayin tsarin karkatar da madafun iko don bai wa sassa daban-daban na kasar nan damar zama nasu.

Don haka, a kasancewar Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa dan shiyyar Arewa, ana sa ran Kudu za ta fitar da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar bisa tsarin da aka yi a jam’iyyar tun 1999.

Saraki ya fito daga Arewa ta Tsakiya kuma ya taka rawar gani a nasarar da Jam’iyyar PDP ta samu a babban taronta na kasa a bara.

A matsayinsa na Shugaban Kwamitin Sulhu na Jam’iyyar PDP ta Kasa, ya zaga ko’ina a Najeriya, inda ya hada kan ’ya’yan jam’iyyar da ke fada da juna gabanin babban taron.

Ana ganin tamkar wannan tsari na shiyya-shiyya ba zai kasance abu mai kyau ba ga Saraki.

Har yanzu dai ba a fitar da tikitin takarar Shugaban Kasa a badi ba, amma shugabannin siyasa da sauran masu ruwa-datsaki daga yankin Kudu sun yi ta yunkurin cewa ya kamata yankin ya samar da wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnonin Kudu 17 da kungiyoyin siyasa da suka hada da Afenifere da Ohanaeze da Kungiyar Kare yankin Neja Dalta (Pan Niger Delta Forum) da Kungiyar Al’ummar Tsakiyar Najeriya (Middle Belt Forum) sun dage cewa sai dai mulki ya koma Kudu a badi.

A kwanakin baya, wani shugaba daga yankin Kudu-masoKudu, Cif Edwin Clark ya bukaci masu son takarar Shugaban Kasa daga Arewa su hakura su yi watsi da wannan ra’ayi domin samun hadin kan kasa.

Ya ce, “Tsarin mulkin PDP kuma bisa yadda aka gudanar da babban taron jam’iyyar, a yanzu lokaci ne da Kudancin kasar nan ya kamata ya samar da Shugaban Najeriya a badi, bayan kammala wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari na shekara takwas.

In ba haka ba, wannan tamkar neman ta da hargitsi ne, wanda kan iya haifar da wargajewar kasarmu mai daraja.”

Sai dai dattijo, Alhaji Tanko Yakasai, ya mayar wa Cif Clark martani, inda ya roke shi da ya daina kawo kalaman barazanar wargajewar kasar nan.

Yakasai mai kimanin shekara 90 a duniya, ya gargadi Clark game da yin irin wannan barazanar. Idan dai za a iya tunawa, Yakasai ya goyi bayan yunkurin ’yan Kudu na samar da Shugaban Kasar.

“Ina ganin a shekarunmu, ya kamata mu guji yin barazana a duk lokacin da muke tattaunawa a kan al’amuran kasa.

“Abin da ake sa ran mutane su koya daga irin shekarunmu shi ne samar da shugabanci ta hanyar ba da shawara da kuma gyara duk wani kuskure da muka gano matasan kasar nan sun tafka a yayin gudanar da zabubbukan kasa.

“Ba a tsammanin wata barazana daga manyan kasa a kowace kasa. Illa kawai su koyar da tsarin shugabanci na kwarai da daidaitawa, da jagoranci mai ma’ana,” inji Yakasai.

Shi kuwa Saraki bai nuna karayarsa ba duk da cewa yankin Arewa ta Tsakiya ne ya samar da Shugaban Jam’iyyar ta Kasa, ya ce hakan bai hana duk wani wanda ya cancanta daga kowane shiyya tsayawa takarar Shugaban Kasa a badi ba.

“A kan batun shiyya-shiyya, jam’iyyar ta bayyana karara a duk tarurrukan da muka yi cewa duk da cewa mun rarraba mukaman ofishin jam’iyyar bisa shiyyoyi, hakan ba ta hana duk wanda yake da muradin neman takarar Shugaban Kasa ba. Abin da muke nema shi ne mafi kyan dan takara da zai ci iya cin zabe,” inji Saraki.

Tuhumce-tuhumce

Zarge-zarge da tuhuma sun mamayetsohon Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Saraki. Laifuffukan cin hanci da rashawa sun samo asali ne tun lokacin da yake rike da mukamin darakta a rusasshen Bankin Société Générale Bank Nigeria (SGBN) da Gwamnan Jihar Kwara, sannan kuma Shugaban Majalisar Dattawa.

An fara shari’arsa ce a lokacin da ya zama Shugaban Majalisar Dattawa a kan dan takarar da Jam’iyyar APC a lokacin ta so ya zama Shugaban Majalisar, wanda wannan lamari ya harzuka shugabannin Jam’iyyar APC. Tun bayan rantsar da Saraki a watan Yunin 2015 a matsayin Shugaban Majalisar Dattawan, Saraki ya tsunduma cikin rikicin da ya dade a cikinsa har ya kai ga karshen wa’adinsa a majalisar.

An zarge shi da hada baki da wadansu masu rike da mukamai a Majalisar Dokoki ta Kasa don “canja dokar Majalisar Dattawa ba bisa ka’ida ba da nufin ya samu nasarar zama shugaban majalisar.”

’Yan sanda sun binciki lamarin kuma bisa sakamakon binciken da shawarwari, an gurfanar da Saraki da Mataimakinsa Ike Ekweremadu da tsohon Akawun Majalisar Dattawa, Efeturi da tsohon Akawun Majalisar Dokoki Ta Kasa, Alhaji Salisu Maikasuwa da laifin yin jabun dokar, aka gurfanar da su a gaban wata babbar kotu a Abuja, inda suka musanta zargin da ake yi musu.

A shekarar 2015, Hukumar Da’ar Ma’aikata (CCB) ta shigar da kara a gaban kotu kan laifuffuka 13 da ake zargin Saraki da yin karya ta wajen bayyana kadarorinsa, karar da ta kai har Kotun Koli, wadda a shekarar 2018 ta wanke shi daga tuhumar da ake yi masa.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta zargi daraktocin SGBN da aka rushe da karkatar da kudaden masu hannun jari. A watan Yulin 2021, EFCC ta tabbatar da cewa an gayyaci Saraki domin amsa tambayoyi kan zargin almundahana da karkatar da kudade.

Daga baya Saraki ya kai Hukumar EFCC wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja domin hana hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bincike shi kan zargin da ya ce yana daga cikin tuhumar da a baya aka shigar da shi a gaban Kotun Da’ar Ma’aikata (CCT).

Hukumar EFCC ta kuma nemi a karbe gidajen Saraki na Legas da ya saya a kan Naira biliyan 1.09, wadanda hukumar ta ce an saye su ne da haramtattun kudaden da ake zargin an sace su ne daga asusun Jihar Kwara. Amma Babbar Kotun Tarayya da ke Legas a karkashin jagorancin Mai shari’a Mohammed Liman ta yi watsi da wannan tuhuma a watan Maris din 2021.

Matsalar Shiyyar Arewa ta Tsakiya

Masu fashin baki na ganin ko da PDP ta bar takarar neman tikitin Shugaban Kasa a bude, zai yi wahala Saraki ya iya shawo kan na kusa da shi da kuma ’yan uwansa daga Arewa saboda ya fito daga tsirarun kabilun Arewa.

A cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara), Saraki ya cancanci ya nemi kujerar Shugaban Kasa.

Ya fito ne daga Jihar Kwara, jihar da ke shiyyar Arewa ta Tsakiya mai fama da rikici a tsakanin kabilar Yarbawa na Arewa.

Kwara, kamar sauran jihohin Arewa ta Tsakiya, ana ganin ba ta da wani muhimmanci a siyasar Arewa, sai dai kawai ta samu alfarmar kasancewa a matsayin daya daga cikin jihohin da ake kira jihohin Arewa 19.

Rikicin Jihar Kwara ya fito fili ne a lokacin da Saraki ya sha kaye a zaben fid-da-gwanin dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2011.

Shigar da sunan Saraki cikin masu neman ra’ayin ’yan Arewa da aka jera don tantancewa a matsayin dan takara daga Arewa, wanda Malam Adamu Ciroma ya jagoranta an ganin tamkar wasan yara ne, saboda ganin bai isa ya wakilci Arewa ba.

An ruwaito cewa mahaifinsa, Dokta Olusola Saraki ya fuskanci irin wannan hali, lamarin da ya kai shi ga kafa kungiyarsa ta Arewa, bayan da ya fice daga Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) kan rarrabuwar kawuna.

Sai dai wata majiya ta kusa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ta ce kasancewar ya fito daga Arewa ta Tsakiya na daya daga dalilan da za su taimaka wajen cimma burin Saraki.

“Kasancewarsa daga Arewa ta Tsakiya abin alfahari ne gare shi, ba illa kamar yadda wadansu ke cewa. Ya fito daga tsakiyar kasar nan.

“Shugabancinsa zai kawo karshen duk wata baraka da ke kasar nan tare da hada kan kowa. Idan Jam’iyyar PDP ta ba shi tikitin takara.

“Takararsa za ta samu karbuwa a tsakanin dukkan manyan kabilun kasar nan, Yarabawa da Hausawa da Ibo, tsirarun kabilu za su gan shi a matsayin daya daga cikinsu.

“Yana da jinin Fulani da Yarbawa,” inji majiyar, wadda take da kwarin gwiwar cewa Saraki zai iya samu n tikitin Jam’iyyar PDP.