✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023: Sarkin Musulmi da CAN sun sa hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya

Sun sanya hannun ne a birnin Washington na Amurka

Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), sun sanya hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya gabanin babban zaben 2023.

Yarjejeniyar dai ana sa ran ta samar da zaman lafiya da kawar da fitina ta fuskar addini a lokacin zaben na badi.

Manyan masu fada a jin biyu sun sa hannu ne a wani taron koli na kasa da kasa kan wanzar da ’yancin addini da wata gidauniyar samar da zaman lafiya da hadin gwiwar wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam guda 70 suka shirya.

A gudarnar da taron ne a birnin Washington na kasar Amurka.

A wata sanarwa da CAN ta fitar a ranar Laraba a Abuja wacce Shugabanta, Mista Ayokunle ya sanya wa hannu ta ce, bangarorin biyu sun yi alkawarin yin aiki tare da gujewa tashi hanakali.

Sun kuma amince su rungumi tattaunawa tare da gina mabiyansu a kan hakuri da juna domin wanzar da zaman lafiya.

“Na san akwai Musulmi da Kiristoci ’yan Najeriya da yawa da ke kyamar tashin hankali, kuma suke bukatar samar da zaman lafiya su da ’yan uwansu da kuma dangi kamar yadda muke a da,” inji Ayokunle na kungiyar CAN.

Sanarwar ta kuma ce kungiyar da kuma Sarkin Musulmin za su yi tsayuwar daka don ganin an yi zabe na gari mai cike da adalci.