✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023 zai raba gardama kan salon mulkin APC a Najeriya —Atiku

Ya ce zaben zai yi alkalanci kan salon mulkin APC

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce zaben 2023 zai zama raba gardama dangane da ayyukan da gwamnatin APC ta yi wa kasa a tsawon lokacin da ta yi rike da mulki.

Atiku ya ce abin damuwa ne yayin da jama’a ke cikin jimami da bakin cikin mummunan harin da aka kai a garin Owo na Jihar Ondo, amma APC ta kasa soke liyafar da ta shirya wa ’yan takararta na Shuagaban Kasa a wannan rana.

Cikin sanarwar da ya fitar ta hannun kakakinsa, Paul Ibe, Atikun ya ce duka yadda aka zubar da jinin masu ibadar da ba su ji ba, ba su gani ba a Jihar Ondo, wannan bai hana shugabannin APC haduwa ba a Abuja don yin shagalinsu wanda hakan ya yi nuni da rashin tausayin halin da kasa ke ciki.

Ya ce, “Yana da muhimmanci a tambayi masu jan ragamar shirya babban taron APC kan dalilin da ya sa suka sanya lokacin taron a ranar aiki, wanda ko shakka babu hakan zai shafi harkokin kasuwanci a cikin Babban Birninin Tarayya.

“Yayin da suke shigo Birnin Tarayyar, dole daliget su fuskanci kalubalen cunkoson ababen hawan da neman shan mai a gidajen mai da kuma rashin wutar lantarki.

“Ya kamata daliget din APC su sani an kawo su Abuja ne ba don komai ba, sai don raba gardama dangane da ayyukan da jam’iyyar ta gudanar a tsakanin shekaru bakwai da suka gabata,” inji Atiku.