✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Abuja: Dan siyasa ya kashe mai kada kuri’a

Wani magoyin bayan jam'iyyun da ke takara a zaben kananan hukumomin Abuja ya kashe wata mata tana kokarin kada kuri'a a ranar Asabar.

Wani magoyin bayan jam’iyyun da ke takara a zaben kananan hukumomin Abuja ya kashe wata mata a lokacin da take kokarin zuwa kada kuri’a a ranar Asabar.

Matar mai matsakaicin ta gamu da ajalinta ne bayan mutumin, wanda magoyin bayan daya daga cikin manyan jami’iyyun da ke fafatawa a zaben ya kade ta da babur dinsa a yayin da take tsallaka titi.

Ya kade matar ne a lokacin da take kokarin tsallaka titi zuwa inda za ta jefa kuri’a a rumfar zaben da ke kusa da Ofishin Gidan Waya na yankin Karu a Karamar Hukumar Birnin Abaja (AMAC) da misalin karfe 10 na safe.

Shaidu sun ce mutumin da ya kade matar ya rika yin tukin ganganci tamkar wanda ya yi shaye-shaye yana kuma ta daga tutar jam’iyyarsa kafin ya yi kan matar da babun din nasa.

Kade matar da ya yi ke da wuya, mutane da suka fito zaben suka yi maza suka kama shi suka mika wa hannun jami’an tsaron da ke kula da zaben.

A jajibirin zaben, Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja ta takaita zirga-zirgar ababen hawa, amma awanni kadan bayan nan ta sassauta dokar tare da kira ga mazauna da su kasance suna gudanar da harkokinsu cikin bin doka da oda.

Daga baya, a cikin dare, ta sake fitar da wata sanarwar takaita zirga-zigar ababen hawa, bisa hujjar cewa ta samu bayanai cewa zauna-gari-banza na neman amfani da damar su tayar da fitina.