✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a girke jiragen yaki 3 da ’yan sanda 34,500 a zaben Anambra

Za a tura horarrun karnuka don sa kafar wando daya da masu neman hana zaben.

Za a tura jiragen yaki uku da ’yan sanda 34,587 domin tabbatar da tsaro a lokacin zaben gwamnan jihar Anambra da za a gudanar a wata mai zuwa.

Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ne ya ba da umarnin tura su a ranar Alhamis a yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba, 2021.

Ya ce ’yan sandan da za a tura sun hada da jami’ai na musamman, jami’an fikira, da sauransu don tabbatar da isasshen tsaro a jihar duba da yadda ’yan kungiyar awaren Biyafara ta IPOB take neman tayar da zaune tsaye a yayin zaben.

Baba ya bayyana hakan ne a Abuja, a taron kwamishinonin ’yan sanda, inda ya ce an tura jiragen yaki uku zuwa jihar ta Anambra domin yin shawagin sintiri a lokacin zaben.

Kazalika, ya ce za a tura horarrun dabobbi da za su taimaka wa jami’an da aka tura wajen dakile duk wani yunkuri na tayar da zaune tsaye ko kuma hana gudanar zabe cikin lumana.

“Muna ci gaba da yin hadin gwiwa da hukumar zabe (INEC), don ganin an gudanar da sahihin zabe kuma cikin lumana.

“Don haka mun aike da jami’an tsaro domin tabbatar da ganin an samu cikakkacen tsaro, tare da dakile duk wata barazana a lokacin zaben,” inji Sufeto Janar na ’Yan Sandan.

Aminiya ta rawaito yadda Sufeton Janar din na ’yan sanda ya jadadda cewa samar da tsaro a jihar Anambra da ma Najeriya baki daya shi ne abin da rundunar ’yan sanda ta sa a gaba.

Har wa yau, ya ce duk kwamandan da ya kasa aiwatar da aikin da aka bayar kamar yadda ya bada umarni za a hukunta shi.