✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Anambra: Jami’in INEC ya tsere da takardun sakamakon zabe guda 42

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dakon sakamakon karshe.

A daidai lokacin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben Gwamnan Jihar Anambra, wani jami’in Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), ya tsere da takardun sakamakon zaben guda 42.

Jami’in hukumar, wanda shi ne mai kula da tattara zabe a Karamar Hukumar Idemili ta Kudu a Jihar, Dokta Gabriel Odorshi ne ya sanar da hakan a hedkwatar hukumar da ke birnin Awka, babban birnin Jihar yayin aikin tattara sakamakon zaben na karshe ranar Lahadi.

Dokta Gabriel, wanda kuma malami ne a Jami’ar Kalaba, ya ce a sakamakon hakan, dole ba a iya gudanar da zabe ba a yankunan da abin ya shafa.

Dan takarar jam’iyyar APGA, kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Farfesa Charles Soludo ne dai ya lashe zaben Karamar Hukumar ta Idemili ta Kudu.

Ya sami kuri’u 2,312, inda ya doke Valentine Ozigbo na jam’iyyar PDP wanda ya sami kuri’u 2,016 da kuma Andy Uba na APC wanda ya sami 1,039.

Har yanzu dai ana ci gaba da tattara sakamakon sauran Kananan Hukumomin kafin a sanar da wanda ya lashe zaben.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, dan takarar jam’iyyar APGA ne ke kan gaba a Kananan Hukumomi 12 daga cikin 21 da ke Jihar.