✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Anambra: Mun magance matsalar BVAS —INEC

INEC ta ce za a ci gaba da tattara sakamakon zaben ranar Lahadi.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa ta shawo kan matsalar da aka samu na na’urar tantance masu zabe ta BVAS a zaben gwamnan Jihar Anambra.

Kwamishinan Zaben Jihar Anambra, Dokta Nkwachukwu Orji, ne ya sanar da haka ranar Asabar a babban ofishin INEC da ke garin Awka, a yayin jawabinsa na uku kan zaben.

Ya kuma sanar da cewa za a ci gaba da tattara sakamakon zaben a ranar Lahadi da safe a cibiyar tattara sakamakon zaben da ke hedikwatar hukumar da ke jihar.