✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023: Tarnakin da zai dabaibaye Atiku

Manyan abubuwan da za su kawo wa Atiku tarnaki a neman takararsa na shuaban kasa a 2023

Shin zaben badi na iya kasancewa dama ta karshe ce ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa na 11, Alhaji Atiku Abubakar, kan burinsa na zama Shugaban kasar da tafi yawan bakaken fata a duniya?

Alhaji Atiku, ya yi yunkurin ganin ya hau kujerar har sau biyar, ba tare da samu nasara ba, sannan ana sa ran zai sake nema a badi wanda za ta kasance damarsa ta karshe ganin kamar wannan ne zangon karshe.

Fitaccen dan jaridar nan, Cif Raymond Dokpesi, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar, ya fara rangadin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, domin nema wa gwanin nasa goyon bayan al’ummar kasar nan a wannan Jamhuriya ta Hudu.

Atiku, wanda ya taba tsayawa takarar Gwamnan Jihar Adamawa a 1990 da 1997, a 1998, an zabe shi a matsayin Gwamnan Jihar, sai dai kafin a rantsar da shi, sai tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya dauke shi a matsayin wanda za su yi takarar zaben Shugaban Kasa a 1999, hakan ya sa ya zamo daya daga cikin manyan ’yan takarar da ake ganin za su gaji Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a badi.

Atiku wanda ya taba fafatawa da Cif MKO Abiola da Ambasada Baba Gana Kingibe a zaben neman tikitin takarar Shugaban Kasa na tsohuwar Jam’iyyar SDP a 1993, akwai tarnaki iri-iri da ake ganin za su kawo masa cikas na cimma burinsa na samun nasara a zaben Shugaban Kasa na badi.

Karba-karbar shugabanci

Akwai tsammanin cewa mulki zai koma Kudu ne a badi bayan Shugaba Muhammadu Buhari, dan Arewa ya kammala shekara takwas a kan karagar mulki.

A bara, gwamnoni 17 a karkashin Kungiyar Gwamnonin Kudancin Najeriya (SGF), sun dage cewa dole ne Shugaban Kasa na gaba ya fito daga yankin.

Sun samu goyon bayan wasu kungiyoyi daga yankin da suka hada da Afenifere, Ohanaeze Ndigbo da Pan-Niger Delta Forum (PANDEF), wadanda suka tabbatar da cewa yin hakan shi ne zai tabbatar da adalci.

Wadansu gwamnoni da jama’a daga Arewa ma sun nuna goyon bayansu ga wannan ra’ayi.

Ta yaya Atiku zai shawo kan mutanen Kudancin Najeriya su manta da maganar takara ta koma Kudu, su daina tunanin karba-karba?

Ta yaya zai sa al’ummar yankin su zabe shi, duk da cewa ana ganin Atiku na iya samun mafi yawan kuri’u daga Arewa a badi?

Sai dai Dokpesi na ganin cewa bai kamata Jam’iyyar PDP ta rudu da tsarin jam’iyya mai mulki ba a kan tikitin takarar

Shugaban Kasa, yana mai cewa ai APC ta fitar da dan takara daga Arewa a shekarar 2015, lokacin da PDP ta fitar da dan takararta daga Kudu.

 “A PDP kuna sane da cewa Shugaba Obasanjo ya cika shekara takwas a matsayin dan Kudu, Sai Umaru Musa ’Yar’aduwa, dan Arewa ya gaje shi.

“’Yar’aduwa ya yi mulki na shekara biyu da rabi, sannan Jonathan ya karasa ragowar wa’adinsa, sannan ya sake yin shekara hudu, a jimlatance Jonathan ya yi shekara shida.

“Kuma tun a wancan lokacin ba mu samu dan takara daga Arewa ba. Don haka, har yanzu Arewa tana cikin rashi idan za a duba ta,” inji shi a wata hira da jaridar Daily Trust a kwanakin baya.

Cif Dokpesi ya yi alkawari a kwanan baya cewa idan aka zabi Atiku zai yi mulki na tsawon shekara hudu ne kawai, wanda hakan zai share fagen samar da Shugaban Kasa daga Kudu musamman Kudu maso Gabas a shekarar 2027.

Shin wannan tunani zai yi tasiri ga mafi yawan ’yan Najeriya a zaben badi?

Dan takara a koyaushe

Tsohon Mataimakin Darakta a Hukumar Kwastam ta Kasa, ana kallon Atiku a matsayin dan takara a koyaushe saboda ya dade yana takarar inda ya yi yunkuri sau biyar bai samu nasara ba.

A 1993 Atiku ya nemi takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar SDP, inda MKO Abiola ya kayar da shi a zaben fid-da-gwani.

Ya tsallake duk wani siradi da Shugaban Kasa na wancan lokaci Obasanjo ya kawo masa, inda ya kaddamar da tsayawarsa takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar

AC a shekarar 2007.

Amma ya sha kaye, bayan marigayi tsohon Shugaban Kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa na Jam’iyyar PDP ya samu nasara, sai Muhammadu Buhari na Jam’iyyar ANPP ya zo na biyu, inda Atiku na Jam’iyyar AC ya zo na uku.

Aiku ya sake komawa Jam’iyyar PDP kuma ya fito takara a zaben fid-da-gwani na jam’iyyar, inda ya sha kasa a hannun Shugaba Kasa na wancan lokaci Dokta Goodluck Jonathan a shekarar 2010.

A shekarar 2014, ya koma Jam’iyyar APC gabanin zaben Shugaban Kasa na 2015, inda ya fafata a zaben fid-da- gwani na Shugaban Kasa, sai dai ya sha kaye a hannun Buhari.

A shekarar 2017, ya koma PDP kuma ya samu tikitin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar a zaben 2019, inda ya sake shan kaye a hannun Shugaba Buhari mai ci.

Masu fashin baki suna ganin ya kamata Atiku ya huta ya mara wa wani baya a cikin harkokin siyasarsu.

A ’yan kwanakin bayan nan daya daga cikin masu magana da yawun Kungiyar Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar a zaben 2019, Kassim Afegbua, ya bukaci Wazirin na Adamawa da kada ya mayar da kansa “Dan takarar Shugaban Kasa a koyaushe.”

Ta yaya Atiku zai iya gamsar da ’yan Najeriya cewa takararsa ta Shugaban Kasa ba burin rayuwa ba ce, soyayya ce ta gaskiya ga kasa da al’umma?

Shekaru

Duk da cewa Atiku bai nuna wata alamar yana fama da wata matsala ta kiwon lafiya ba, ko kadan, amma dai shekaru ba jiransa za su yi ba, musamman a daidai lokacin da ake begen ganin an samu shugabanni matasa sun karbi ragamar tafiyar da harkokin kasa.

Idan aka zabi Atiku zai cika shekara 77 a duniya wata shida kafin ranar 29 ga Mayun badi.

Seyi Makinde, daya daga cikin gwamnoni kuma shugaba a Jam’iyyar PDP a kwanakin baya ya bukaci ’yan Najeriya su yi zabe cikin hikima a badi ta hanyar zabar mutanen da suke da karfin jiki da kaifin tunani don tafiyar da al’amuran kasar nan.

“Mun ga dattijai da yawa da suke son mulkin kasar nan suna da shekara 75 ko 78. Ina son su sake tunani, kuma ina gaya wa mutanen Jihar Oyo da Najeriya cewa duniya fa ba sauki ba ce.

“Muna cikin kakar zabe, a gaskiya kuma abin da zan ce mana a matsayinmu na jama’a shi ne, mu zabi mutanen da suke da kazar-kazar da za su iya yi wa kasa hidima,” inji Gwamnan na Jihar Oyo.

Shin wannan sako ne kai-tsaye ga Atiku mai shekara 75?

Tuhuma kan dukiya

Ana kallon Alhaji Atiku a matsayin daya daga cikin ’yan siyasar kasar nan masu dukiya.

Sai dai abin bakin ciki, a Najeriya ana kallon ’yan siyasa a matsayin mahandama.

Wannan ya sa masu sukar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar suke tababa da kuma tuhumar tushen dukiyarsa.

Duk da cewa ba a same shi da laifin cin hanci da almundahana ba, amma ana ganin matsalar cin hanci da almundahana za ta iya zame masa kalubalen da ya kamata ya shirya tsame kansa daga ciki kafin yakin neman zaben badi.

Masu suka kan yi saurin yin tsokaci kan wasu kalamai marasa dadi da kuma zargin cin hanci da almundahana da tsohon ubangidansa, Obasanjo ya yi masa.

Atiku, wanda a kwanakin baya ya janye hannu daga babban kamfanin hada-hadar kayayyaki na Intels Nigeria Limited, kamfanin da ya kafa, dole ne ya nemi hanyar da zai bijire wa wannan labari domin ya samu karbuwa a zukatan jama’a.

Gwamnoni 13 na Jami’iyyar PDP ne suka fi kowa karfi a cikin jam’iyyar. Suna kula da tsarin jam’iyyar.

An nuna haka ne a yayin babban taron jam’iyyar da ya gabata, inda suka tabbatar ’yan takararsu ne suka samu mukamai 18 daga cikin 21 ta hanyar sulhuntawa.

Da wannan ne masana ke cewa gwamnonin sun karbe ragamar babbar jam’iyyar adawar kafin zaben badi.

Ana kuma ganin cewa wadannan jiga-jigai suna da karfi sosai wajen fitowa da dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar.

Takwas daga cikin gwamnonin sun fito ne daga Kudu kuma suna cikin kudirorin da Kungiyar Gwamnonin Kudu suka amince da su cewa dole ne yankin ya samar da Shugaban Kasa a badi.

Ko a zaben 2019, sai a kusan karshe, bayan da kusoshin jam’iyyar suka sa baki, sannan Atiku ya doke Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, wanda shi ne dan takarar da gwamnonin PDP suke bukata, a zaben fid-da-gwani na jam’iyyar da aka gudanar a Fatakwal, sannan ya samu tikitin takarar Shugaban Kasa.

Domin nuna rashin jin dadinsu a kan matakin, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da Ayodele Fayose na Ekiti, a fili suka nuna kuri’arsu, inda suka zabi Tambuwal duk da irin umarnin da masu fada-a-ji na jam’iyyar suka bayar.

Shin Atiku zai iya jan hankalin Wike da sauransu, su goyi bayan burinsa a wannan karo? Ana ganin wannan a matsayin wani babban tarnaki a takararsa.

Sai dai kuma wani jigo a jam’iyyar ya ce, “Atiku zai samu goyon bayan gwamnonin wajen samun tikitin takarar.

“’Yan siyasa suna da dabara da kuma wayo wajen hada lissafi.

“A cikin gwamnonin wane ne ya bayyana ko ya nuna sha’awar yin takarar a karkashin jam’iyyar? Dan takarar Arewa shi ne kawai wanda zai iya kayar da Jam’iyyar APC mai mulki,” inji shi.

Ya yi nuni da cewa abin da gwamnonin Kudu daga jam’iyyar suke yi shi ne yadda daya daga cikinsu zai zama Mataimakin Shugaban Kasa ta hanyar tabbatar da cewa Atiku bai yanke shawarar daukar wanda za su yi takara tare ba kamar yadda ya yi da Peter Obi a 2019.

Mai taimaka wa Atiku kan Harkokin Yada Labarai, Paul Ibe, ya ce Najeriya tana fuskantar barazanar rashin tsaro da rashin aikin yi da sauran kalubale.

Don haka, ya ce ana bukatar shugabancin da ba a saba gani ba a yanayi da ba a saba gani ba.

“Abin da ke da muhimmanci shi ne kowa ya fahimci inda muke a tarihinmu-muna fuskantar kalubale mai girma na tarihi.

“Lokacin da kuka fuskanci yanayi na ban-mamaki, akwai bukatar wanda zai iya ba da jagoranci mai inganci kuma abin mamaki.

“Shugabancin da zai fara aiki tun daga ranar farko, shugabancin da zai hada kan kowa da kowa.

 “Shin Atiku yana da wadannan dabi’u? Eh, shi gogaggen shugaba mai sadaukarwa.

“Shugaban da bai nuna bambanci da zai iya hada kan kowa da kowa, mai samar sda aikin yi, wanda ya nuna kwarewa a harkokin kasuwancinsa da sauransu.

“Kuma shi mai hangen nesa ne,” inji shi.