✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Edo: ’Yan APC sun sauya sheka zuwa PDP

Jam’iyyar PDP ta karbi karin wasu ‘yan Jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa cikinta a Jihar Edo, gabanin zaben gwamnan jihar na ranar 19…

Jam’iyyar PDP ta karbi karin wasu ‘yan Jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa cikinta a Jihar Edo, gabanin zaben gwamnan jihar na ranar 19 ga Satumba.

Masu sauya shekar a Karamar Hukumar Owan ta Gabas sun koma PDP ne a ranar Alhamis, domin mara wa Gwamna Godwin Obaseki baya a zaben da ke tafe, bayan ficewarsa daga APC.

Da yake karbar su, Shugaban PDP a yankin, Sanata Yisa Braimoh ya ce hakan shaida ce a kan gamsuwar mutanen jihar da ayyukan da gwamnan ya yi a wa’adinsa na farko.

Ya ce daga dawowar gwamnan PDP zuwa lokacin, “jam’iyyar ta yi wa sabbin mutane 3,000 rajista a karamar hukumar. Da a yau za a yi zabe a jihar da za mu lashe a gundumominmu da kashi 85%”, inji Sanata Braimoh.

Shi ma da yake bayani, Obaseki ya ce gwamnatinsa za ta bayar da muhimmanci ga cigaban rayuwar dan Adam.

Ya ba da tabbacin fara aikin titin Ivbiaro zuwa Warrake a watan Oktoba, saboda muihmmacinta ga manoma.