✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Ekiti: SDP ta yi watsi da sakamako, za ta garzaya kotu

Abun kunya ne yadda jam'iyyar APC ta rika sayen kuri'u a bainar jama'a.

Jam’iyyar SDP ta yi fatali da sakamakon zaben gwamnan Jihar Ekiti da Hukumar Zabe ta kasa INEC ta bayyana sakamakonsa.

A ranar Asabar ce aka gudanar da zaben gwamna a Jihar Ekiti, inda kafin wayewar gari ranar Lahadi, INEC ta sanar da dan takarar jam’iyyar APC, Abiodun Oyebanji a matsayin zakara bayan ya kayar da sauran ’yan takara 15 da jimillar kuri’u 187,057 da ya samu.

Sai dai jam’iyyar SDP ta bakin wakilinta a matattarar sakamako da kidayar kuri’un zaben, Barista Owoseni Ajayi, ya yi barazanar cewa za su garzaya Kotun Sauraron Korafe-Korafen Zabe wajen neman hakki.

Da yake zantawa da Aminiya a matattarar sakamakon zaben da ke Ado Ekiti, Barista Ajayi, ya kwatanta zaben da “abin kunya” yana mai cewa sayen kuri’u da rikici ne ya mamaye shi.

“Wannan zabe abin kunya ne ga Najeriya duba da yadda APC ta rika sayen kuri’un mutane a bainar jama’a.

“Wannan abin takaici ne, yadda aka rika sayen imanin mutane saboda yadda talauci ya yi katutu a Jihar – ko a zabubbukan fitar da ‘yan takarar Shugaban Kasa na APC da PDP mun ga haka.

“Sannan kuma da gangan wasu ‘yan barandan gwamnati suka rika tayar da hargitsi yayin gudanar da zabe a wuraren da SDP ke da rinjaye.

“Saboda haka za mu kai kukanmu gaban Kotun Sauraron Korafe-Korafen Zabe, don ba za mu amince da wannan ba”, inji Mista Ajayi.

Barista Ajayi ya bayyana cewa dan takarar jami’iyyar SDP, Segun Oni ya tsarkaka daga sayen kuri’u domin ya sha kausasa harshe da gardadin aikata wannan abun kunya a lokuta daban-daban.

“Ko kadan ba mu yi sayen kuri’a ba, kuma idan akwai mai shaida a kan mun aikata hakan yana iya gabatar da ita a matsayin hujja.”

Wakilinmu ya ruwaito cewa Barista Ajayi ya ki amincewa ya sanya hannu a kan takarda mai dauke da sakamakon zaben da aka tattara.

A nata bangaren, wakilin jam’iyyar APC, Honarabul Kayode Babade wanda ya musanta zargin Barista Ajayi, ya ce batun sayen kuri’u bakon lamari ne a wurinsu da ba su san da zaman shi ba.

“Amma duk wani wanda yake zarginmu da aikata ba daidai ba, yana iya gabatar da shaidarsa.

“Jama’a sun fito sun zabi ra’ayinsu saboda mun gabatar musu da dan takara na gari, wanda ya shirya yi musu aiki tukuru.

“Saboda haka daman ai duk wata jam’iyya da bai wuce cikin mako biyu ta soma shirye–shiryenta babu yadda za a yi ta iya cin wani zabe,” a cewar Babade.

Honarabul Babade ya kuma yi wa al’ummar Ekiti alkawarin cewa ba za su kunyata ba a karkashin jagorancin Oyebanji, yana mai cewa gogewarsa za ta tabbatar an sharbi romon dimokuradiyya.

Segun Oni, dan takarar jam’iyyar SDP ne ya zo na biyu a zaben da kuri’a 82,211 amma bai samu ko da karamar hukuma daya ba.

Mista Oni, wanda ya taba zama a kujerar gwamnan Jihar ta Ekiti, yana gaban dan takarar jam’iyyar PDP, Bisi Kolawole, wanda ya samu kuri’a 67,457.