✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Faransa: Macron da Le Pen za su tafka muhawara

Za a yada zazzafar muhawarar da za gudanar a ranar Laraba kai-tsaye a talabijin

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da abokiyar hamayyarsa mai tsatsauran ra’ayi, , Marine Le Pen, za su tafka muhawarar da za a watsa ta gidan talabijin a ranar Laraba, inda kowannensu ke fatan jan ra’ayin masu kada kuri’ar da ba su yanke shawarar wanda za su zaba ba.

Yanzu haka dai shugaba Macron ke kan gaba a zaben shugabancin kasar bayan da ya lashe zagayen farko da fiye da kashi 27 na kuri’ar da aka kada.

Sai dai masana siyasa sun gargade shi da ya kauce wa tafka kuskuren yin sakaci kan burinsa na zarcewa zuwa wa’adi na biyu, a yayin muhawarar da za a fafata da Marine Le Pen.

Wasu zabukan jin ra’ayin jama’a da aka gudanar sun yi hasashen cewa shugaba Macron zai samu nasarar lashe zagaye na biyu na zaben da zai gudana nan da kwanaki hudu, da ratar kusan kashi 10 na kuri’ar da za kada, wato maimaicin abin da ya faru a zaben 2017.

Sai dai masu jefa kuri’ar da har yanzu ba su yanke shawara kan inda za su karkata ba ka iya sauya alkaluman zaben.

Bayanai dai sun ce a bana jagorar ’yan adawa Marine Le Pen, ta maida hankali kan yin shiri na musamman game da muhawarar da za ta yi, don kauce wa abin da ya faru shekara biyar da suka gabata, lokacin da rashin shirinta kan muhawarar ya taka rawa wajen shan kaye da ta yi a hannun Mista Macron.

Muhawarar kai-tsaye tsakanin ’yan takarar shugabancin Faransa ta kasance al’adar siyasa a kasar tun daga 1974, lokacin da dan jam’iyyar gurguzu Francois Mitterrand ya yi takara da Valery Giscard d’Estaing (Valeri Giskar Distar).