✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben fid da gwanin PDP: Daliget 2 ne suka zabi Shehu Sani a Kaduna

Tun kafin zaben dama ya ce ko sisi ba zai ba daliget ba don su zabe shi

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattijai, Shehu Sani, ya sami kuri’a biyu kacal a zaben fid da gwanin jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, saboda bai ba daliget ko sisi ba.

Idan za a iya tunawa, dai zargin kan yadda daliget ke amsar makudan kudade a zaben fid da gwanin bana na karuwa, in da har aka samu wasu da ba su samu nasara ba ke neman a dawo musu da kudaden da suka bayar.

Sai dai tun gabanin zaben, an jiyo Sanata Shehu Sanin na cewa ko sisi ba zai biya kowanne daliget ba don ya zabe shi, kuma a haka ya shiga zaben, aka samu daliget biyu kacal da suka zabe shi.

A wani rubuta da yayi a shafinsa na Twitter, Sanatan ya ce, “An kammala zaben fid da gwanin PDP, Hon Isah Ashiru ne ya lashe, kuma ina taya shi murna.

“Kuri’u biyu da na samu daga daliget ina godiya gare su, domin ban ba su ko sisi ba,” inji shi.

Tuni dai aka ayyana tsohon dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Makarfi da Kudan, Isah Ashiru Kudan a matsayin wanda ya lashe zaben kuma wanda zai yi wa jam’iyyar takara a zabe mai zuwa.

Ko a zaben shekara ta 2019 ma shi ne ya tsaya wa PDP takara, amma ya yi rashin nasara a hannun Gwamna mai ci, Nasiru El-rufa’i.