✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Ghana: An rantsar da kwamatin zaman lafiya

Majalisar dinkin Duniya ta taya mambobin kwamitin tabbatar da zaman lafiya a kasar Ghana murna na sake rantsar da su da Shugaban kasa John Mahama…

Majalisar dinkin Duniya ta taya mambobin kwamitin tabbatar da zaman lafiya a kasar Ghana murna na sake rantsar da su da Shugaban kasa John Mahama ya yi ranar Talata.
Jakadan Majalisar a yankin Yammacin Afirka Muhammad Ibn Chambas ya ce yarjejeniyar Kumasi da ’yan takaran kujeran shugaban kasa suka kulla gabanin zaben shekarar 2012, ya taimaka ainun wurin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
Ya ce saboda haka ne akwai bukatar sake kirkiro wata yarjejeniyar gabanin babban zaben bana.
Da yake sake rantsar da majalisan zaman lafiyar wacce mambobinta suka hada da shugabannin addinai daban-daban. Har ila yau, an bayyana cewa Rabaran Emmanuel Asante ne zai jagoranci majalisar.
Shugaba Mahama ya ce babban abin da ke gabansu shi ne yaki da tallauci. Ya ce “aikin da ke gabanmu ba na kabilanci ne, ko addini ko yaki da abokan adawan siyasa ba ne.”
Daga nan shugaban ya nanata bukatar da zaman lafiya a gabanin da lokaci da kuma bayan babban zaben kasar wanda za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.