✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Ghana: Obasanjo ya gargadi Akufo-Addo da Mahama

Ina yi wa 'yan takara da al'ummar kasar Ghana fatan Alheri, a yayin babban zaben kasar, cewar Obasanjo.

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya gargadi ’yan takarar shugabancin kasar Ghana game da rikici a yayin babban zabe mai zuwa a ranar 7 ga watan Disambar 2020.

Obasanjo ya yi wannan kira ne cikin wata wasika da ya aike wa da ’yan takarar jam’iyyun National Democratic Congress (NDC) da New Patriotic Party (NPP), inda ya ce yana da kyau su fahimci juna, domin samun zaman lafiya.

A shekara ta 2016 Akufo-Addo, ya kayar Mahama a zaben shugabancin kasar da ya gudana, yanzu ma za su sake karawa a babban zabe mai zuwa.

Yayin da zaben yake kara tunkarowa, Obasanjo ya bukaci ’yan takarar da su rungumi zaman lafiya, domin kauce wa tashin hankali a yayin zaben mai zuwa.

Daga karshe tsohon shugaban kasar, ya yi fatan alheri ga ’yan takarar shugabancin kasar Ghana da kuma samun zaman lafiya mai dorewa.