Daily Trust Aminiya - Zaben Ghana: ‘Yan takara sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya
Subscribe

Shugaban Ghana da John Mahama

Zaben Ghana: ‘Yan takara sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya

’Yan takarar shugabancin kasar Ghana a karkashin manyan jam’iyyun NPP mai mulki da NDC mai adawa, sun rattaba hannun kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a zaben da za a gudanar ranar 7 ga watan Disamba.

’Yan takarar jam’iyyun biyu sun hada da Shugaban Kasa mai ci, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo da Tsohon Shugaban Kasa, John Dramani Mahama.

Zaben Ghana: Obasanjo ya gargadi Akufo-Addo da Mahama

Musulmin Ghana sun yi tattakin neman a yi zabe lafiya

Zaben Ghana: An rantsar da kwamatin zaman lafiya

Duk ’yan takarar biyu sun yi alkawarin za su yi bakin kokarinsu domin gani ba a samu hatsaniya ba lokacin zaben da kuma bayan an kammala shi ranar litinin mai zuwa.

Hukumar Habaka mulkin siyasa ta kasar Ghana (IDEG) ce ta kirkiri zaman domin tabbatar da ’yan takarar biyu sun bi hanyar da ta dace wajen neman gyara idan basu gamsu da zaben da aka gudanar ba.

Da yake jawabi a yayin zaman, John Dramani Mahama ya ce zai yi iya kokarin ganin an aiwatar da zaben cikin lumana.

Sai dai kuma ya ce tarzomar da aka samu kwanakin kadan da suka wuce a karkashin mulki Akudo-Addo ka iya zama barazana ga zaben.

“A yanzu ne rayuwar mafi yawan al’umma kasar nan ta dogara ga zabe, muna bukatar hukumar zaben ta yi adalci don ganin an samu sahihin sakamako da kowa zai aminta da shi.

“Har yanzu ba mu manta abin da ya faru da Ayawaso West Wuogon ba, saboda gwamati ba ta hukunta wanda ya ci zarafin Dan majalisa ba tare da raunata mutane da dama.

“Wannan mummunar ranar ce ga tarinin siyasar kasar nan,” inji Mahama.

A nashi jawabin, Shugaban kasa Nana Akufo-Addo ya bayar da tabbacin cewar hukumar zaben za ta gudanar da sahihin zabe kuma cikin lumana.

Ya ce, babban abinda jam’iyyarsa ta NPP ta ke bukata shi ne a gudanar da zaben da kowa zai gamsu da shi ba tare da tarzoma ba.

“Muna fatan ayyukan alheri da mu ka yi za su al’umma kasar su kara zabarmu.”

“Burinmu shi ne, mu samu kuri’un da za mu yi wa abokan hammayarmu kayin raba-ni-da-yaro, ina kuma mai bayar da tabbacin za mu rugumi kaddarar abin da sakamakon zaben ya bayyana.”

Aminiya ta ruwaito cewa ’Yan takarar biyu kuma za su yi hadin gwiwa domin ganin an kawar da kungiyar ’Yan banga kafin a gudanar da zaben.

Wadanda suka halarci zaman sun hada da Shugaban alkalan Ghana, Anin Yeboah da Babban limamin Ghana, Sheikh Osman Nuhu Sharubutu, da Shugaba Hukumar samar da zaman lafiya ta kasar, Rebranded da dai sauransu.

More Stories