✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamna: Mun shirya samar da tsaro a Kano —’Yan Sanda

'Yan sandan sun ce za su sa kafar wando daya da duk wanda ke shirin tada yamutsi a jihar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce a shirye take ta samar da tsaro a lokacin zaben gwamna da ’yan majalisar dokoki da za a yi a jihar a ranar 11 ga watan Maris. 

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Manman Dauda, ya ce ’yan sanda da sauran jami’an tsaro za su samar da tsaro a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar.

Dauda, ya ce tuni aka bayar da cikakken umarnin gudanar da aiki ga kwamandojin yankin da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro kuma sun shirya tsaf don kare masu kada kuri’a da jami’an INEC a lokacin zabe da kuma bayansa.

“Ina ba da tabbacin kashi 100 cikin 100 ga duk mazauna jihar masu bin doka da oda, cewa za su iya gudanar da aikinsu ba tare da wata barazana ga rayuka da dukiyoyi ba a ranar 11 ga Maris,” in ji shi.

Dauda ya ce matakan tsaro da aka sanya za su bai wa masu kada kuri’a damar shiga dukkan harkokin zabe ba tare da barazana ba.

“Za mu samar da yanayi mai kyau don bai wa mazauna Kano damar zaben shugabannin da suke so a cikin yanayin siyasa na lumana.

“Muna aiki tare da sauran hukumomin tsaro don samar da aminci da kuma magance duk wata barazana a lokacin zabe da kuma bayansa.”

Kwamishinan ya shawarci mazauna jihar da kada su firgita da yadda za su jami’an tsaro suna aiwatar da aikinsu a lokacin zabe.

“Ba za mu amince da duk wani aiki da zai iya kawo rudani kafin zabe, lokacinsa ko bayansa ba; duk wani mutum ko kungiya da aka samu sun ki bin umarni za a kama su kuma a gurfanar da su a gaban kuliya,” in ji shi.

Kwamishinan ya yi kira ga iyaye da kada su bari a yi amfani da ’ya’yansu wajen yin bangar siyasa domin duk wanda ya shiga hannu, zai yaba wa aya zaki.