✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben Gwamnan Ekiti: Fayose da Fayemi za su sake gwada kwanji

Fayose da Fayemi sun dade suna adawa; Fayose ne ya fara Gwamna, aka tsige shi, Fayemi ya ci zabe a karo na farko.

A ranar Asabar ce za a fafata zaben Gwamnan Jihar Ekiti, inda ’yan takara 16 ne za su fafata domin maye gurbin Gwamnan Jihar, Kayode Fayemi.

Daga cikin fitattun ’yan takarar akwai, Biodun Oyebanji na Jam’iyyar APC da Olabisi Kolawole na Jam’iyar PDP da tsohon Gwamnan Jihar, Segun Oni na Jam’iyyar SDP da Ranti Ajayi na Jam’iyyar YPP da Oluwole Oluyede na Jam’iyyar ADC.

Sai dai duk da cewa akwai fitattu a cikin ’yan takarar, inda akwai tsohon Gwamna, amma an fi mayar da hankali kan ’yan takara biyu na PDP da APC, musamman ganin iyayen gidansu na siyasa tsofaffin abokan hamayya ne.

Dan takarar APC

Dan takarar APC, Biodun Oyebanji, tsohon Shugaban Ma’aikata ne na Gwamna Fayemi, sannan ya taba rike Kwamishinan Tattalin Arziki da Kasafi a karkasin gwamnan.

Ya yi aiki da Gwamna Kayode Fayemi tun a zangon mulkinsa na farko kafin tsohon Gwamnan Jihar, Ayodele Fayose ya doke shi a lokacin da ya nemi komawa kujerar.

Sannan da ya dawo a karo na biyu bayan Fayose ya kammala wa’adinsa, ya ci gaba da aiki da shi.

Shi ne Sakataren Gwamnatin Jihar Ekiti kafin ya sauka domin neman takarar kujerar Gwamnan.

Dan takarar PDP

Shi kuwa, Olabisi Kolawale wanda tsohon Kwamshinan Muhalli ne a zamanin Fayose shi ne ya doke ’yan takara ciki har da tsohon Mataimakin Gwamna da tsohon Gwamna domin samun tikitin takarar a PDP bayan Ayodele Fayose ya nuna goyon bayansa gare shi.

Takun sakar Fayemi da Fayose

Fayose da Fayemi sun dade suna adawa, musamman kasancewar Fayose ne ya fara Gwamna, aka tsige shi, Fayemi ya ci zabe a karo na farko.

Fayose ya dawo, ya doke Fayemi, sannan bayan ya kammala wa’adinsa, Fayemi ya sake dawowa, inda ya doke dan takarar PDP na lokacin, Farfesa Kolapo Olusola Eleka ya koma domin yin wa’adi na biyu.

Yanzu kasancewar su biyun duk sun kammala wa’adi bibbiyu da doka ta tanada, sai suka tsayar da yaransu, inda masu sharhi kan harkokin siyasa suke ganin za a dora fafatawar ce daga inda suka tsaya.