✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamnan Gombe: Jam’iyyu 5 sun mara wa dan takarar AA baya

Kwana biyu kafin zaben gwamna, jam’iyyun siyasa 5 a Jihar Gombe sun hade wajen goyon bayan takarar Burgediya Nuhu Millier (mai ritaya) na Jam'iyyar AA.

A lokacin da zaben gwamna da na yan majalisar dokokin jiha ya rage kwanaki uku, wasu jam’iyyun siyasa 5 a Jihar Gombe sun hade wajen goyon bayan takarar Burgediya Nuhu Millier (mai ritaya) na Jam’iyyar AA.

Jam’iyyun sun hada AAC, APM, APP, APGA da kuma Accord Party (AP).

Shugaban Jam’iyyar APGA na jihar, Muhammad Mahdi Doho, ya ce jam’iyyun da magoya bayansu za su mara wa Nuhu Millier baya ne don ganin ya kada jam’iyyar APC mai mulki a zaben da ke tafe na ranar asabar.

A cewarsa, Millier gogaggen dan siyasa ne mai karamci wanda idan aka zabe shi zai ciyar da Jihar Gombe gaba ya kuma samar da ribar mulkin dimokuradiyya.

Mahdi ya kara da cewa kafin daukar wannan matsaya, sai da suka tattauna suka kuma nemi shawarin masu ruwa da tsaki.
Shugaban Jam’iyyar AA na jihar, ya ce wannan hadaka za ta kara bai wa jam’iyyar damar lashe zaben.

Auwal, ya yi kira ga al’ummar jihar da su fito su zabi dan takarar nasu domin cancanta.

Shi ma a nasa bangare Burgediya Nuhu Millier, ya yaba wa jam’iyyun bisa karamci da mara masa baya da suka yi wanda a cewar sa hakan na nuna cewa ya cancanci ya zama gwamnan jihar Gombe.

Janar Millier, ya hori magoya bayansa da su kara nemo masa jama’a, sannan ya roki matasa da su rungumi zaman lafiya su kuma tsaya tsayin daka dan ganin an jefa kuri’a kuma an zabe shi.