✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kaduna: PDP ta lashe akwatin da El-Rufa’i ya kada kuri’a

Sakamakon dai ya nuna PDP ce ta lashe akwatin a zaben Kansila da na Ciyaman.

Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Kaduna ta lashe akwatin da Gwamnan Jihar, Nasir El-rufa’i ya kada kuri’arsa yayin zaben Kananan Hukumomin Jihar na ranar Asabar.

Sakamakon, wanda Hukumar Zabe ta Jihar Kaduna Mai Zaman Kanta (KADSIECOM) ta fitar a akwatun mai lamba 001 a Unguwar Sarki da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa ya nuna cewa ta sami kuri’a 86 daga cikin 159 da aka jefa a zaben Shugaban Karamar Hukumar.

A nata bangaren, jam’iyyar APC mai mulki kuwa ta sami kuri’a 62 ne, yayin da APP ta sami daya, ZLP ta sami biyar, PRP hudu.

Kazalika, PDP ta kuma sami kuri’a 100 daga cikin 162 da aka kada a zaben Kansila, yayin da APC ta sami 53, ZLP biyu, PRP ma biyu, NNPP daya sai kuma BP mai kuri’a hudu.

Jami’in akwatin, Muhammad Sani ne ya sanar da sakamakon zaben.

Tun da farko dai Gwamnan El-rufa’i ya shaida wa ’yan jarida bayan kada kuri’arsa cewa ya kirkiro da tsarin zabe da na’ura mai kwakwalwa ne saboda jama’a su zabi abin da suke so.