✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kananan Hukumomi ya kankama a Ondo

Zaben Shugabannin Kananan Hukumomi ya kankama a Jihar Ondo, bayan tantance masu jefa kuri’a a safiyar Asabar 22 ga Agusta, 2020. Wasu rahotanni sun nuna…

Zaben Shugabannin Kananan Hukumomi ya kankama a Jihar Ondo, bayan tantance masu jefa kuri’a a safiyar Asabar 22 ga Agusta, 2020.

Wasu rahotanni sun nuna cewa zuwa karfe 10 na safiya aka fara tantance masu zabe a wasu rumfuna duk da cewa a wasu wuraren an samu jinkiri fiye da haka.

Bullar annobar COVID-19 ta sa aka dage zaben da aka shirya gudanarwa a watan Afrilu, kafin a watan Yuli Shugaban Hukumar Zaben Jihar Ondo, Yomi Dinakin ya sanar cewa za ayi shi a ranar 22 ga Agusta.

A wasu rumfuna da majiyarmu ta ziyarta an samu jinkirin isar kayan zabe.

Wani da takarar Kansilan Jam’iyyar APGA a gundumar Ayeotoro, a Karamar Hukumar Ilaje Agere Olowoloba ya ce zuwa lokacin ba dukkannin rumfunan zaben yankin ne suka samu kayan zabensu ba.

“Rumfar zabe shida ce a Mazabar Ayetoto amma biyar daga cikinsu ne aka kai kayan zabe”, inji shi a lokacin.

A watan Oktoba ne za a gudanar da zaben gwamnan jihar wanda jam’iyyu 17 za su fafata, ciki har da gwamna mai ci Rotimi Akeredolu.