✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kano: APC tana gaban NNPP da kuri’a 1113

Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta Kasa (INEC) reshen Jihar Kano ta fara tattara tare da sanar da sakamakon zaben gwamna na aka kada a…

Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta Kasa (INEC) reshen Jihar Kano ta fara tattara tare da sanar da sakamakon zaben gwamna na aka kada a jihar a jiya Asabar.
Kafin Hukumar ta tafi hutu ta sanar da sakamakon kananan hukumomi 19.
Aminiya ta rawaito cewa Jamiyyar NNPP ta sami nasarar lashe kuriun kananan hukumomi 10 da suka hada da Karamar Hukumar Rano da Rogo da Wudil da Karaye da Minjibir da Albasu da Gabasawa da Ajingi da Kibiya da Gezawa da Tudunwada.
Haka kuma Jamiyyar APC ta sami nasarar lashe kuriun kananan hukumomin Makoda da Kunci da Tsanyawa da Shanono da Bagwai da Kabo da Warawa da Dambatta.
A gaba dayan sakamakon da aka fadi Jamiyyar APC tana da kuriu 328,040 yayin da Jamiyyar NNPP ta sami kuriu 326,927. Hakan ya sa aka sami tazarar kuriu 1113 tsakanin jamiyyun biyu da ke hamayya da juna a jihar.