Zaben Kano: babu wani dalilin soke zabe – APC | Aminiya

Zaben Kano: babu wani dalilin soke zabe – APC

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya ce, babu wani dalilin soke zaben jihar da ake gudanarwa a jihar.

Shugaban APC ya mayarwa jam’iyyar  adawa ta PDP martani, yayin da suka  bukaci a soke zaben Gwamnan jihar da ake yi yau.

Alhaji Abdullahi, ya watsi da zargin da jam’iyyar PDP ke yi akan tura `yan daba rumfunan zabe. Ya kuma ce babu wani dalilin soke zaben jihar ganin yadda zabukan ke gudana a jihar.