✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Nijar: Namadi Sambo zai jagoraci masu sa ido na ECOWAS

Najeriya ta jaddada goyon bayanta ga makwabciyarta, Jamhuriyar Nijar

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Muhammad Namadi Sambo zai jagorancin tawagar Kungiyar ECOWAS wurin sanya idanu kan zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki a Jamhuriyar Nijar da za a gudanar a watan Disamban da muke ciki.

Namadi Sambo wanda ya bakunci Shugaba Buhari a Fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata, ya ce tuni suka fara gudanar da taruka da shugabanni daban-daban a kan zaben da ke tafe.

Ya yi alkawarin cewa ECOWAS za ta tabbatar an yi sahihin zabe na adalci cikin kwanciyar hankali a Jamhuriyar Nijar, duk da kalubalen siyasa da shari’u da rashin tsaro da ake fuskanta a halin yanzu.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, ya kuma taya Shugaba Buharu murnar nasarar ceto Daliban Makarantar GSSS Kankara da aka yi garkuwa da su; da kuma cikar Buharin shekara 78 a makon jiya.

Yayin da yake gabatar da nasa jawabin, Buhari ya kara jaddada wa Jamhuriyar Nijar goyon bayan Najeriya a gare ta.

Ya yaba wa Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou, saboda rashin yi wa kundun tsarin mulkin kasar katsalandan don kara wa kansa wa’adin mulki bayan ya kammala wa’adin zangon mulkinsa biyu.

“Na fito ne daga garin Daura, kilomita kalilan zuwa kasar Nijar, akalla na san wani abu a kan kasar.

“Shugaban Kasar dattijo ne, kodayaushe muna tattaunawa da shi; Ya kammala iya adadin zangon mulkin da tsarin mulkin kasar ya tanada.

“Zan yi magana da Shugaban Kasa kan ba wa kasar dukkannin gudunmawar da ya kamata a bayar,” inji Buhari.