✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben Ondo: Akeredolu ya lashe kananan hukumomi 10

Akeredolu na jam'iyyar APC na kan gaba sannan Eyitayo Jegede na PDP

Dan takarar jam’iyar APC a zaben Gwamnan Jihar Ondo, ya lashe kananan hukumomi 8 cikin 10 da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana sakamakonsu.

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu shi ne kan gaba da kuri’u 62,795 bayan da Hukumar Zaben ta fitar da sakamakon kananan hukumomi 10 cikin 18 da ake da su a jihar.

A daya bangaren dan takarar babbar jam’iyar adawa ta PDP Eyitayo Jegede ya lashe ragowar kananan hukumomi biyu cikin 10 da Hukumar Zaben ta  sanar da sakamakonsu.

Akeredolu dan takarar jam’iyyar APC ya samu jimullar kuri’u 152,248 yayin da Eyitayo Jegede ya samu 89,453.

Ga dai sakamakon kananan hukumomi goman kamar yadda Hukumar Zabe ta kasa ta fitar

 1. Karamar Hukumar Owo
 • APC: 35,957
 • PDP: 5,311
 1.  Karamar Hukumar Ondo ta Gabas
 • APC: 6,486
 • PDP:4,049
 1.  Karamar hukumar Akoko Arewa maso Yamma
 • APC: 15,806
 • PDP:10,320
 1. Karamar Hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma
 • APC: 21,322
 • PDP:15,055
 1. Karamar hukumar Akoko Arewa ta Gabas
 • APC: 16,572
 • PDP: 8,380
 1. Karamar hukumar Irele
 • APC: 12,643
 • PDP: 5,493
 1. Karamar hukumar Ile Oluji
 • APC: 13,278
 • PDP:9,231
 1. Karamar hukumar  Ifedore
 • APC:9,350
 • PDP:11,852
 1. Karamar hukumar Akure North
 • APC: 9,546
 • PDP: 12,263
 1. Karamar hukumar Idanre
 • APC: 11,286
 • PDP: 7,499