✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben PDP: An umarci daliget su yi zabe da ‘Unity List’

PDP ta shirya jerin sunayen tun kafin babban taronta na kasa da ke gudana.

Masu fada a ji a jam’iyyar PDP sun umarci daliget da su kada kuri’a daidai da jerin sunayen ‘Unity List’ a babban taron jam’iyyar na kasa da ke gudana.

Majiyoyinmu a hedikwatar PDP sun shaida mana cewa jerin sunayen  an fitar da shi ne tun kafin zuwan babban taron jam’iyyar da ake gudanar da zaben.

Wakilinmu bai samu ganin kwafin jerin sunayen ba, amma majiyarmu ta ce, “A babban taron jam’iyyar na baya an yi amfani da ‘Unity List’ a wannan ma za a yi amfani da shi.”

‘Unity List’ din dai na dauke da sunaye da mukaman wadanda idan suka ci zaben za su zama mambobin Kwamitin Gudanarwar na Kasa (NWC) a jam’iyyar.

Duk da cewa an cimma daidaito a kan yawancin mukaman da ke  kwamitin gudanarwar na kasa, hakan bai samu ba a kan wasu, wanda ya sa aka fitar da jerin sunayen domin saita wa daliget alkiblar yadda za su yi zaben.

Idan ba a manta ba a 2017 PDP ta yi amfani da ‘Unity List’ wanda ya kai ga samar da Kwamitin Gudanarwa na Kasa karkashin jagorancin Prince Uche Secondus.