✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben shugabannin PDP a Jihohi: Wasu na kuka, wasu na murna

A wasu jihohi an tashi lafiya a wasu kuma an samu tashin hankali.

A ranar Asabar da ta gabata ce Jam’iyyar PDP ta gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar a wasu jihohi, daga cikinsu akwai jihohin Adamawa da Oyo da Kwara.

Yayin da aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali a jihohin Adamawa da Kwara, an samu hatsaniya a Jihar Oyo, inda wadansu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai wa wani babban jami’in jam’iyyar, mai suna Mista Omolaja Alao hari a wurin zaben da aka gudanar a Cibiyar Jogor da ke hanyar Ring Road a Ibadan, babban birnin jihar.

Lamarin ya rutsa da shugaban gunduma ta 1 a Karamar Hukumar Ibadan ta Arewa maso Gabas.

An dai kai masa harin ne a bakin babbar kofar shiga wajen zaben.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an zabi Mista Michael Okunlade a matsayin shugaba a wani taro na daban da wani bangare mai biyayya ga tsohuwar Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai, Misis Mulikat Akande-Adeola ya gudanar.

A jawabinsa na amincewa da zaben, Mista Okunlade, ya yi alkawarin kwantar da hankalin dukkan ’ya’yan jam’iyyar don yin aiki tare wajen ci gabanta Kazalika bangaren da Gwamna Seyi Makinde yake jagoranta, Sanata Hosea Agboola da Ogunwuyi sun gudanar da nasu zaben, wanda ya samar da Mista Dayo Ogungbenro a matsayin shugaba.

Da yake jawabin amincewa da kama ragamar shugabancin, Mista Dayo Ogungbenro ya gode wa dukkan ’yayan jam’iyyar domin amincewar da suka yi na ba zabarsa a wannan mukami, tare da yin alkawarin cewa babu wani shugaba ko bawa a lokacin mulkinsa.

Daga Jihar Legas rahotanni sun ce an dakatar da yin zaben sakamakon tashin hankalin da ya barke a wurin taron a Dandalin Tafawa Balewa.

Aminiya ta gano cewa ana gab da fara kada kuri’a ce, sai wadansu ’yan daba suka mamaye wurin, wanda hakan ya haifar da yamutsin da ta kai ga dakatar da taron.

Ganin yadda lamarin ya so ya kazance ne, sai Shugaban Kwamitin Shiray Zaben, Injiniya Johnson Abounu ya sanar da dage taron.

Sai dai a wata sanarwa da Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar mai barin gado, Mista Taofik Gani ya fitar ya zargi Jam’iyyar APC mai mulki a jihar da ltayar da zaune-tsaye domin yin kafar ungulu ga taron nasu.

Daga Jihar Kwara Jam’iyyar PDP ta gudanar da taron lami lafiya, inda aka zabi sabbabin shugabanninta.

An zabi tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Babatunde Mohammed a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

Alhaji Babatunde Mohammed ya maye gurbin Injiniya Kola Shittu, wanda ya rike wannan mukami na fiye da shekara uku.

Jam’iyyar ta amince da yarjejeniya wajen zaben sababbin shugabannin nata.

Tuni aka rantsar da sabbabin shugabannin, wadanda tsohon Kwamishinan Sadarwa Alhaji Babatunde Ajeigbe, ya rantsar da su.

A jawabin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, kuma jigo a Jam’iyyar PDP a Kasa, Sanata Bukola Saraki, ya ce taron da aka yi shi cikin lumana alama ce ta nuna cewa jam’iyyar a shirye take ta karbe madafun iko a jihar.

Ya taya shugabanni da mabiya murna ganin an gudanar da taron cikin lumana ta hanyar amincewa da tsarin da aka amince da shi.

Tun farko, Shugaban Kwamitin Zaben da ya je daga Abuja, Mista John Aparachi, ya ce, “Yana da kyau yadda al’ummar Jihar Kwara suka yi, domin sun yi daidai da abin da Shugaban Jam’iyyar ta Kasa ya nemi a yi na gudanar da komai lafiya.”

Wakilai 2,614 ne suka yi zabe a Adamawa

A Adamawa wakilai 2,614 ne suka halarci taron inda aka zabi sababbin shugabannin jam’iyyar a jihar.

An sake zaben Barista Tahir Shehu, a matsayin Shugaban Jam’iyyar a jihar.

Wakilai sun dawo da Barista Shehu da mambobin zartarwarsa da yawa yayin taron.

Wakilan sun ce hakika taron jam’iyyar da aka gudanar a Dandalin Ribadu a Yola shi ne mafi tsari bayan zuwan dimokuradiyya a 1999.

Shugaban Kwamitin Zaben na Jam’iyyar PDP kuma Gwamnan Jihar Bayelsa, Mista Douye Diri, ya ce sha’awar da mambobin jam’iyyar suka yi ga taron ya tabbatar da ingancin jagorancin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.

Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar ta fadada ayyukanta a Adamawa da irin tsarin da ya dace, na ganin yadda za ta kawar da Jam’iyyar APC mai mulki a zaben Shugaban Kasa mai zuwa.

A jawabin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, kuma dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya yaba da ayyukan Gwamna Ahmadu Fintiri tare da bayyana shi a matsayin jagoran jam’iyyar, inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa PDP za ta kwace mulki daga hannun APC a 2023.

Da yake jawabi, Gwamna Ahmadu Fintiri ya yi alkawarin ci gaba da jajircewa don inganta rayuwar jama’a da ci gaban jihar, yana mai cewa kyawawan halayen da aka nuna a taron sun nuna cewa PDP ce ke kan mulki.

Daga Muhammad Aminu Bashi da Jeremiah Oke, Ibadan da Mumini AbdulKareem, Ilorin da Abdullateef Aliyu, Legas da Kabiru R. Anwar, Yola.