✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaftarewar kasa: Wadanda suka mutu sun kai 84 a Brazil

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa zaftarewar kasa a yankin.

Gwamnan Paulo Camara na Jihar Pernambuco da ke Arewa maso Gabashin Brazila a kasar Brazil,  ya tabbatar da rasuwar mutum 84 bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya haddasa zabtarewar kasa.

Camara ya ce, “Mun san cewa da farko an samu tsaiko wajen bayar da agaji, amma yanzu ana yin aiki yadda ya kamata.

“Na yi magana da dukkan masu unguwanni don kafa tsarin aiki domin taimaka wa gwamnati.”

An ayyana dokar ta baci a yankuna 14 da ke kusa da tashar jiragen ruwa ta Recife, hedikwatar Pernambuco.

Camara, ya sanar da bayar da tallafin Dala miliyan 21 ga wadanda abin ya rutsa da su.

A ranar Laraba ne aka fara samun guguwa mai karfin gaske a yankin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 79 a karshen mako.

A yankin na Recife, sama da milimita 200 na ruwan sama ne ya sauka a cikin sa’a 24, in ji gwamnatin Jihar ta Pernambuco.

Mutum 56 ne suka bace a sanadin iftila’in, yayin da wasu kusan 4,000 suka rasa muhallansu.

Ministan raya yankin, Daniel Ferreira, ya ce “Ko da yake ruwan saman ya dauke yanzu, muna sa ran za a samu karin ruwa a kwanaki masu zuwa.

“Don haka abu mafi mahimmanci shi ne samar da hanyoyin kariya.”