✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zahra Buhari ta ce ba mahaifinta ba ne matsalar Najeriya

Ta ce gano maboyan kayan tallafin COVID-19 ya nuna cewa ba Buhari ba ne matsalar Najeriya

Diyar Shugaba Buhari, Zahra Buhari-Indimi ta ce yadda mutane suke bankado maboyan kayan tallafin COVID-19 ya nuna cewa ba mahaifinta ba ne matsalar Najeriya.

Zahra ta wallafa hakan ne a shafinta na Instagram.

“Yanzu mutane sun tabbatar da cewar Buhari ya raba isassun kayan tallafi, don haka ba shi ne matsalar Najeriya ba”, inji Zahra Buhari.

A kwanaki biyu da suka gabata dubban ’yan Najeriya sun yi ta fasa rumbunan da gwamnatocin jihohi suka adana kayan tallafin COVID-19 suna kwashewa.

Jihohin da aka fasa inda aka killace kayan tallafin sun hada jihar da Legas, Filato, Kaduna, Osun, Kwara, Adamawa da Adamawa da sauransu.

A wasu jihohin an samu kayan tallafin da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin raba wa mabukata a gidajen ’yan siyasa.

Wannan ya jawo sanya dokar hana fita a wasu jihohi, domin guje wa afka wa dukiyoyin al’umma kamar yadda hakan ta faru a wasu jihohi.