✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zakaran Gasar Olympic din guragu ya yi karar hukumar gidan yarin Afirka ta Kudu

Dan kasar Africa ta kudu zakaran gasar olympics Oscar Pistorius, wanda kotu ta yanke wa hukuncin shekara 13  ya kai hukumar gidan yarin kasar kara…

Dan kasar Africa ta kudu zakaran gasar olympics Oscar Pistorius, wanda kotu ta yanke wa hukuncin shekara 13  ya kai hukumar gidan yarin kasar kara a kotu.

Tsohon zakaran ya kai hukumar kula da gidajen yari ta kasar ne gaban alkali yana bukatar kotu ta tilasata mata zaman sauraron neman afuwa a bisa tsarin doka.

Lauyansa Julian Knight ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da kamfanin diallancin labarai na AFP a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa, sun shigar da kara ne domin Osca ya cancanci a yi masa afuwa bisa la’akari da shekarun da ya yi a jarun.

A cewarsa. “karar ba ta na nufin dole sai an yiwa Oscar afuwa ba ne, amma a yi zaman sauraron cancantrasa shi mu ke nema”.

Sannan ya ce, Kotun ba ta sa ranar sauraron karar ba, daga nan kuma Lauyan bai kara cewa komai a hirar.

Osca Pistorious shi ne gurgu maras kafafu na farko da ya shiga gasar tseren wasannin Olympics na nakassasu, ya kuma ciwo wa kasarsa Afirka ta Kudu lambobin yabo a shekarun 2011 da 2012.

Wata kotu a kasar ta yanke masa hukuncin shekarun 13 ne a gidan yari sakamakon samun sa da laifin kisan budurwarsa Reeva Steenkamp a shekarar 2013, inda ya harbe ta da bindiga a gidansu, a bisa kuskuren barawo ne, a cewarsa.

A bisa dokar Afirka ta Kudu kafin a yi wa fursuna afuwa, sai ya yi akalla rabin wa’adin hukuncin da kotu ta yanke masa.

Sannan wajibi ne ya kasance laifinsa na farko, an kuma shaide shi da kyakkyawan hali a yayin zamansa.