✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zakaran musabakar Alkur’ani na Duniya ya rasu

Mahaddacin shi ya lashe musabakar Alkur’anin da aka yi a Kasashen Kuwait da Qatar.

Sadiq Abdullahi Umar, matashin da ya wakilci Najeriya a musabakar Alkur’ani a ciki da wajen kasar, ya riga mu gidan gaskiya.

A hirar da Aminiya ta yi da wani dan uwan marigayin mai suna Muhammad Kabiru Makarfi, ya ce “Malam Sadiq ya rasu ne a Kasar Sudan bayan wata ‘yar rashin lafiya kimanin kwanaki 26 da komawarsa daga Kano.

Marigayi Sadiq ya rasu yana shekaru 26 da haihuwa, ya kuma bar mahaifiyarsa da sauran ‘yan uwa da kuma dangi.

Tuni aka yi jana’izarsa a Sudan kamar addinin musulunci ya tanadar.

Kafin rasuwarsa, mahaddacin shi ya lashe musabakar Alkur’anin da aka yi a Kasashen Kuwait da kuma Qatar.

Shi ne kuma zakaran musabakar da aka yi a Kasar Zanzibar a watan Maris na shekarar 2022.

Baya ga wannan, marigayin ya samar da kafofin koyar da karatun Alkur’anin ta intanet a tashar You tube.