✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaman bata-gari a Gombe ya kare —CP Babantunde

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Ishola Babaita, ya gargadi bata-gari da cewa su tattara komatsansu su bar gari don yanzu kam ba su da mafaka…

Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Ishola Babatunde Babaita, ya gargadi bata-gari da cewa su tattara komatsansu su bar gari don yanzu ba su da mafaka a Jihar.

CP Babantunde, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake hira da manema labarai a Hedikwatar ’Yan Sandan a lokacin da ya shiga ofis.

Ya ce ya zo ne domin yi wa Gombe aiki, don haka bata-gari su kwana da sanin cewa daga yanzu ba sani, ba sabo.

A cewarsa, yana da zafi a kan abin da ya danganci cin hanci, kuma ko da dan sanda aka kama da laifi, to zai fuskanci fushin hukuma.

Daga nan sai ya nemi hadin kan al’ummar Gombe a manufarsa ta kawo gyara, kuma a matsayinsa na tsohon dan sanda, ba zai bari ’yan ta’adda su kawo wa jama’a matsala ba muddin yana kan kujerarsa.