Zaman diyar Trump a kujerarsa a taron G-20 ya jawo cece-ku-ce | Aminiya

Zaman diyar Trump a kujerarsa a taron G-20 ya jawo cece-ku-ce

Shugaban Amurka Donald Trump ya kare ‘yarsa Ivanka Trump wadda ake ta caccaka saboda ta zauna a kujerar sa a taron G-20 da ya wakana a Hamburg da ke kasar Jamus. A kokarinsa na kare ta, shugaba Trump sai da ya saka shugaban Jamsu Angela Merkel da Chelsea Clinton diyar Hillary Clinton cikin lamarin. A cewarsa “A lokacin da na fita daga cikin dakin taron domin na halarci taro da Japan da wasu kasashe, sai na ce wa Ivanka da zauna a kujerar. Wannan ba wata matsala ba ce. Angela Merkel ma ta yarda.” Kamar yadda Trump a wallafa a shafinsa a twitter. Trump ya qara da cewa da ace Chelsea Clinton diyar Hillary ce mahaifiyarta ta ce ta zauna mata a kujera, da babu wanda zai yi magana “Inda ace Chelsea Clinton ce ta zauna wa mahaifiyarta a kujera kamar yadda mahaifiyarta ta bayar da kasar mu, labarun karyan zai zama ne a zabi Chelsea a matsayin shugaban qasa,” inji shi. Jim kadan bayan shugaban kasar ya wallafa rubuce-rubucen nan a shafinsa na Twitter, sai Chelsea Clinton, diyar tsohuwar abokiyar hamayyar shi ta mayar da martani inda ita ma ta wallafa a shafinta na Twitter tana cewa “Ina kwana shugaban qasa. Ba zai taba yiwu wa ba mahaifiyata ko mahaifina wani daga cikinsu ya ce na zauna a kujerar sa. Amma kai da ka ce diyarka ta zauna a kujerar ta ka, shin kai ma ka bayar da kasar mu kenan? Ina fata ba haka ba ne.” inji Chelsea Clinton. A lokacin da ake taron G-20, shugaban ya fita domin ya halarci wani taron, sai aka ga Ivanka ta zauna a kujerar sa a tsakanin shugaban Chana Xi Jinping da Firaministan Birtaniya Theresa May, inda nan take hoton ya kawo cecekuce ganin yadda ta zama mataimakiyar shugaban ba gaira ba dalili.

Merkel ta yi bayani abin da yasa Ivanka ta zauna a kujerar taron, inda ta shaida wa manema labarai cewa “Mutanen taron ne suke amincewa da wanda zai zauna a kujerar duk shugaban da baya nan a lokacin taro,” inji Merkel. “Ivanka tana cikin tawagar Amurka. Wannan abu ne da wadansu tawagar ke yi. Kowa ya san cewa tana aiki a fadar shugaban kasar Amurka, kuma ana saka ta a wasu ayyukan gidan.” Dan uwan Ivanka,

Donald Trump qarami, wanda shi baya cikin tsarin tafiyar da mulkin kasar, wanda kuma a yanzu yake fama da tashi matsalar, yak are ’yar uwarsa inda ya ambace “Mai matukar fasaha da iya magana” sannan daga bisani ya kara da cewa “Idan har sun ji haushi a kan Ivanka ta zauna a kujerar na ’yan mintuna, watakila za su fi yin murna idan aka ce ni ne na zauna na wani zan lokaci