✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaman lafiya zai dawo Najeriya kafin Buhari ya bar mulki — Malami

Ya ce Buhari na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da hakan

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami, ya ba da tabbacin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai dawo da Najeriya kan tafarkin zaman lafiya kafin ya bar mulki a 2023.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Birnin Kebbi, domin taya Musulmi murnar Sallar Layya.

Malami ya ce sam Buhari ba ya barci, ba wai kawai don ganin ya mika mulki cikin ruwan sanyi ba, yana ma kokarin ganin ya kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar kasar.

Ya ce, “Ina so in tabbatar muku da cewa gwamnatin Buhari za ta ci gaba da yin dukkan abin da ya kamata wajen dawo da tsaro a Najeriya.

“Muna addu’ar Allah ya amsa addu’o’inmu, ya dawo da zaman lafiya a Jihar Kebbi da ma kasa baki daya, da kuma tabbatar da mika mulki cikin ruwan sanyi a badi,” inji Malami.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ce dai wa’adin Buhari zai kare na shugabancin Najeriya.

Sai dai kasar na ci gaba da fama da matsalolin tsaro, inda ko a cikin makon nan sai da aka kai wa ayarin Shugaban hari a hanyarsu ta zuwa Daura, sannan aka fasa gidan yarin Kuje da ke Abuja tare da sakin daruruwan fursunoni