✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zambar N12m ta sa an gurfanar da dan shekara 47 a gaban Kuliya

Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa, ta gurfanar da wani mutum mai shekaru 47 a gaban wata Kotu da ke zamanta a Karamar Hukumar Karu ta…

Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa, ta gurfanar da wani mutum mai shekaru 47 a gaban wata Kotu da ke zamanta a Karamar Hukumar Karu ta Jihar.

Kotun yayin zaman da ta gudanar a ranar Talata, an gabatar da mutumin wanda ake zargi da laifin zambar kudi wuri na gugar wuri har naira miliyan 12.

Ana tuhumar mutumin da laifin aikata zamba cikin aminci da yaudara da almundahana, sai dai ya musanta laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Jami’in dan sandan da ya gabatar da karar, Ade Adeyanju, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya karbi kudi naira miliyan 12 da nufin gudanar da harkokin kasuwanci, amma bayan wata uku sai ya dawo da wani bangare na kudin.

Sai dai ya ce bincike ya nuna cewa mutum ya yi bushasharsa ne kawai da kudin ba tare da gudanar da kasuwanci da ya yi ikirari a baya ba, inda a halin yanzu ya yi kememe yayin da aka nemi ya dawo da bashin kudin da ya karba.

Jami’i Ade Adeyaju ya ce, mutumin da aka zambata mai suna Rose Ulekhia wanda mazaunin unguwar Lugbe da ke Abuja shi ne ya yi karar mutumin a caji ofis.

Alkalin Kotun, mai shari’a Anas Mohammed, ya bayar da belin wanda ake zargi kan naira miliyan 13 tare da neman ya gabatar da mutane biyu mazauna yankin da kotun take da za su tsaya masa.

Mai Shari’a Anas ya kuma bukaci mutane biyu da za su tsaya wanda ake tuhuma su kasance sun mallaki wata kadara da ta kai kimar kudin da aka gindaya a matsayin kudin beli ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 24, ga watan Fabrairun 2021.