✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamfara: An dakatar da Sarkin Zurmi kan ayyukan ’yan bindiga

Gwamna Matawalle ya ba da sati uku a kawo rahoton binciken sarkin da ya dakatar nan take.

Gwamnan Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya dakatar da Sarkin Zurmi, Alhaji Atiku Abubakar Muhammad, nan take bisa zargin sa da hannu a ayyukan ’yan bindiga a masarautar.

Matawalle ya kuma ba da umarnin kafa kwamiti mai karfi da zai binciki zargin dakataccen sarkin da hannu wajen karuwar ayyukan ’yan bindiga a yankinsa.

Ya kuma umarci wani hakimi a Masarautar ta Zurmi, Bunun Kanwa, Alhaji Bello Suleiman, ya ci gaba da gudanar da harkokin Masarautar, nan take.

Sanarwar da Mukaddashin Sakataren Gwamnan, Kabiru Balarabe, ya fitar ta ce kwamitin binciken zargin sarkin Zurmi da aka dakatar zai kunshi mutum takwas, karkashin jagorancin Mataimakin Gwamnan Jihar, Ibrahim Wakkala, kuma zai gabatar da rahotonsa cikin mako uku.

Dakatar da Sarkin Zurmi na zuwa ne kimanin sati biyu bayan zargin alaka da ’yan bindiga ya sa Gwamna Matawalle dakatar da Sarkin Dansadau, Alhaji Hussaini Umar da kuma Hakimin Nassarawar Mailayi a Karamar Hukumar Birnin Magaji ta Jihar, Alhaji Bello Wakkala.

A ranar Juma’a rahotanni suka bayyana cewa ’yan bindiga sun hallaka akalla mutum 93 a kauyen Kadawa da ke Masarautar ta Zurmi.

Mazauna sun ce maharan da suka kai harin ranar Alhamis da dare suna magana ne da wani yare da ba na Najeriya ba.

Sun kara da cewa maharan sun yi ta bin mutanen da suka yi yunkurin tserewa daga kauyen suna kashewa.

Aminiya ta kawo rahoto cewa kauyuka biyar ne a Masarautar Zurmi ’yan bindiga suka kai hari tsakanin ranar Alhamis da Juma’a.