✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamfara: Majalisar za ta tsige Mataimakin Gwamna

Ana zargin Barista Mahdi da saba wa kundin tsarin mulki, keta hurumin ofishinsa, da kuma cuwa-cuwa

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta karbi takardar bukatar tsige Mataimakin Gwamnan Jihar, Barista Mahdi Aliyu Gusau, daga mukaminsa.

Mataimakin Shugaban Majalisar kuma Shugaban Kwamitin Majalisa kan Asusun Gwamnati, Musa Bawa Musa, shi ne ya gabatar da takardar bukatar tsige mataimakin gwamnan a zauren majalisar a ranar Juma’a.

Mataimakin Shugaban Majalisar yana zargin Barista Mahdi da saba wa kundin tsarin mulki, keta hurumin ofishinsa, da kuma cuwa-cuwa, laifukan da ya ce kowannensu ya isa a tsige shi daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.
Bayan karbar takardar, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfar, Nasiru Mu’azu Magarya, ya yi alkawarin yin nazari kan zargin tare da daukar makatakin da ya dace daidai da abin da doka ta tanadar.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Barista Mahdi amma abun ya faskara, amma Sakataren Jam’iyyar PDP Reshen Jihar Zamfara, Farouk Ahmad Shattima, ya ce ba za su ce komai ba tukuna, uwar jam’iyyarsu za ta ba da amsar da ta dace a lokacin da ya dace.